Gwamna Bello Mohammed Matawallen Maradun, ya taya iyayen yaran da aka sako wadanda aka sace daga makarantar sakandiren gwamnati ta kimiyya da ke Kankara a jihar Katsina murna, tare kuma da nuna takaici game da maganganun da ake yi na nuna cewa jam’iyyar APC ta taka rawa a jihar Zamfara wajen yaki da ‘yan bindiga a yankin arewa maso yamma. Wannan kuma sune irin bayanan da aka rika yi a baya da aka rika yabo ga gwamnan jihar Katsina, Honorabul Aminu Bello Masari bayan kokarin da gwamna Matawalle ya yi na ceto ‘yan mata 26 wadanda ‘yan bindiga suka sace a karamar hukumar Faskari duk dai a jihar ta Katsina.
Duk da cewa gwamna Bello Mohammed ya ki hada al’amurra da kowa akan wannan al’amari, zarge-zargen na kara yawa. Domin a kore dukkan wadannan tunane-tunane, ya zama dole a bayyana bayanai daki-daki ga kowa.
Abu ne sananne cewa jihar Zamfara ta shiga cikin mummunan yanayi da ‘yan bindiga suka jefata a lokacin APC a gabadaya yankin arewa maso yamma, har sai da gwamna Bello Mohammed ya zo. Shirin sa na zaman lafiya, wanda kuma ya dace da yadda ake yi tsawon zamunna a sassan duniya domin kawo karshen ‘yan bindiga da makamantansu, shi ne shirin da wadanda suka kasa suke ki da kyama domin ba za su iya aiwatar da shirin cikin gaskiya, hakuri da dabaru ba.
A yau, jihar Zamfara tana cikin zaman lafiya fiye da mafi yawan makwaftanta saboda gwamna Bello Mohammed ya kasance shi mai gaskiya ne a cikin al’amurransa, wanda hanya ce wadda za ta iya kawo karshen matsalolin da yankin ke fuskanta.
Bai kamata ba kwata-kwata saboda kawai banbancin siyasa a ce ana danganta zaman lafiyar da Zamfara ke jin dadin samu a yau da kuma yin jigilar ‘yan ta’addan zuwa wasu jihohi domin yi musu ta’addanci ba. Ya kamata dai a sani cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance yana tare da dukkan shirye-shiryen gwamna Matawalle kuma ba sai daya ba ya nuna jin dadinsa ga irin hanyoyin da ya ke bi domin kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a jihar.
Gwamna Bello Mohammed na so ya sanarwa da al’umma cewa shirinsa na amfani da lalama da kuma akasinta wajen kawo karshen ‘yan bindiga ya yi nasara inda aka sasanta da wadanda suka amince da shirin, wadanda kuma basu amince ba aka kawo karshen su inda aka kawo karshen ‘yan bindiga 300 a cikin watanni biyu kawai. Domin haka kuskure ne a bayyana dazukan jihar Zamfara a matsayin wuri amintacce ga masu aikata laifuka. Wannan ma kuma cin zarafi ne kai tsaye ga sojojin Nijeriya wadanda ke karkashin ikon gwamnatin tarayya.
Gwamna Matawalle har wa yau yana kira ga dukkan bangarorin al’umma, musamman wadanda suke a yankin, da su hada hannu waje daya domin samun mafita a maimakon yin tuhume-tuhume ga juna.
Ya zuwa hada wannan rahoto duniyace taima lamarin ca tare da zura idanu da kulle don ganin ya gwamnati za tayi akan lamarin