Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar Da Aikin Titin Koko–Zuru Kan Naira Biliyan 64
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru Kan Naira Biliyan 64

byUmar Faruk
8 months ago
Titin

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya ƙaddamar da aikin shimfiɗa titin Koko zuwa Dabai da ke Ƙaramar Hukumar Zuru, wanda zai ci Naira biliyan 64.

Aikin zai gudana ne ƙarƙashin kamfanoni uku, kuma ana sa ran za a kammala shi cikin watanni 18.

  • Sojoji Sun Ƙwato Makamai, Sun Ci Gaba Da Neman Bello Turji A Zamfara
  • Wa’adin Ficewar Nijar, Mali Da Burkina Faso Daga ECOWAS Ya Cika Yau

Hanyar, wacce ta kai tsawon kilomita 87, ta kasance mallakar gwamnatin tarayya.

Sai dai saboda jinkirin aiki, an soke kwangilar baya, kuma hukumomin tarayya sun bayar da dama ga gwamnatin Kebbi ta ɗauki nauyin aikin, tare da alƙawarin mayar mata da kuɗaɗen da ta kashe bayan an kammala aikin.

Gwamna Nasir ya bayyana cewa, ko da gwamnatin tarayya ta biya ko ba ta biya ba, gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin aikin, ganin yadda titin ke da matuƙar muhimmanci ga al’ummar jihar da ma Nijeriya baki ɗaya.

Ya gargaɗi kamfanonin da suka samu kwangilar da su tabbatar da ingantaccen aiki, tare da jaddada cewa za a hukunta duk wanda ya kasa cika sharuɗan aikin.

Sannan, ya buƙaci direbobin manyan motoci da su guji lodin da ya fi ƙarfin titin domin kare lafiyar matafiya da rage hatsari.

Don haka, gwamnati za ta kafa kwamiti don tabbatar da bin doka da oda a kan titin.

Kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Abdullahi Umar Faruk, ya bayyana cewa kashi 40 na kuɗin aikin an riga an biya.

Ya ce an biya kamfanonin kuɗin kamar haka:

  • Kamfanin ZBBC zai shimfiɗa titin daga Dabai zuwa Mahuta (kilomita 25) a kan Naira biliyan 18.
  • Kamfanin Habib Engineering LTD zai yi aikin daga Mahuta zuwa Marafa (kilomita 25) a kan Naira biliyan 18.
  • Kamfanin GNIC zai yi aikin daga Koko zuwa Marafa (kilomita 37) a kan Naira biliyan 27.

Baya ga titin Koko – Zuru, Gwamna Idris ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar za ta inganta babban asibitin Zuru domin ya zama cibiyar ƙwararru.

Haka nan, a yayin ziyarar godiya da ya kai ƙananan hukumomin Fakai, Sakaba, Danko Wasagu, da Zuru, ya kuma ƙaddamar da wata hanyar karkara mai tsawon kilomita 11 daga Koko zuwa garin Kangin Korama, wanda aikin zai ci Naira biliyan 1.3.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki
Labarai

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu
Labarai

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Alkaluman Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na 2025 Sun Kai Sabon Matsayi

Alkaluman Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na 2025 Sun Kai Sabon Matsayi

LABARAI MASU NASABA

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version