Connect with us

LABARAI

Gwamna Shettima Ya Bayar Da Umurnin Daukar Sabbin Malamai 2,000 A Jihar Borno

Published

on

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ya bayar da umurnin fara daukar sabbin malaman makarantu, domin cike gibin da ake dashi a sabbin makarantu sama da 40 da gwamnatin jihar ta gina, tare da wanda ake dashi a sashen ilimin jihar.
Shugaban hukumar kula da ma’aikatan jihar Borno, Malam Yerima Saleh ne ya bayyana hakan ga manema labarai, a Maiduguri, babban birnin jihar.
Ya ce, tuni ofishin hukumar sa ya tsara fam ga masu sha’awar cika wa. Tare da bayyana cewa, a cikin wannan adadi, za a dauki masu takardar shaidar kammala digiri kimanin 800, wadanda suka karanta darussan kimiyya da lissafi.
Bugu da kari kuma, ya ce sun tsara daukar malaman wadanda suke da shaidar kammala karatun NCE 200, matsayin malamai na din-din-din.
Dadin-dadawa kuma ya ce, an ware guraben mutum 1,000, da suka kunshi tsuffin shugabanin makarantun sakandire, tsuffin malamai da ma’aikatan da suka yi ritaya, wadanda suke da sha’awar ci gaba da koyarwa- domin sadaukarwa, wanda kuma za a rika biyan su alawus mai tsoka.
“daukar sabbin ma’aikatan, hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jihar Borno da bankin duniya tare da kungiyar tarayyar Turai, a matsayin bangaren sake gina yankunan da matsalar tsaro ta tagayyara, wanda Gwamna Shettima ya nemo alfarmar sa”.
“baya ga wannan adadi na malaman makarantu 2,000, akwai karin wasu sabbin ma’aikata da suka kunshi jami’an tafiyar da aikin gwamnati (admin) 100, injiniyoyi guda 100 tare da ma’aikatan jinya da unguwan-zoma da ma’aikatan kiwon lafiya mataki na farko 100, wadanda kuma dukkan su masu shaidar kammala digiri ne- da za a tura wurare daban-daban, a matakin albashi 10 zuwa 13, na matsakaicin ma’aikaci”. Inji shi.
Shugaban hukumar kula da ma’aikatan ya nusar da cewa “a bisa wani rahoton binciken da RPBA ta gudanar, ya nuna cewa matsalar tsaron ta jawo asarar rusa gidaje kimanin 956,453 a jihar Borno, wanda ya doshi kaso 30 cikin dari na gidajen jama’a.
“A hannu guda kuma, wannan rikici na Boko Haram ya rusa ajujuwa 5,335, da ke makarantun firamare 512 da na sakandiri da a manyan makarantu 38.
“Har wa yau, matsalar ta rutsa da cibiyoyin kiwon lafiya 201 da gine-ginen gwamnati 665 tare da wasu hanyoyin raba wutar lantarki kimanin 726. Sauran su kunshi cibiyoyin samar da ruwan sha, da suka hada da riyojin burtsatse, tuka-tuka da tankunan ruwa masu amfani da hasken rana kimanin 1,630 ne suka salwanta.
“Bisa ga wannan yunkuri na gwamnatin Kashim Shettima ta hanyar hada kari da gwamnatin tarayya, kanana da manyan kunkiyoyin bayar da tallafi, zai taimaka gaya wajen farfado da bangarorin more rayuwar jama’ar jihar da dama, musamman bangaren ilimi”. Ya nanata.
Advertisement

labarai