Gwamna Shettima Ya Kaddamar Da Gina Sabbin Gidaje 500 A Borno

Gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima, ya kaddamar da fara gina sabbin gidaje 500, da mayakan Boko Haram suka kona a Gajiram, shalkwatar karamar hukumar Nganzai da ke jihar Borno, a karshen wannan makon.
Karamar hukumar Nganzai, wadda ke da nisan tazarar kilo mita 90 daga birnin Maidugurin jihar Borno, yanki ne wanda ya sha fama da barazanar hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram a baya.
Bugu da kari kuma, garin Gajiram, shi ne mahaifar tsohon shugaban tarayyar Nijeriya, a lokacin mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha.
Da yake dora harsashen tubalin gina sabbin gidajen a garin na Gajiram, Gwamna Shettima, ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta kammala aikin, nan da zawa karshen wannan shekara ta 2018.
Dadin-dadawa kuma, Shettima ya isa garin tare da manyan motocin dakon kaya 16- cike da kayan abinci da tufafi domin raba wa yan gudun hijira, ta hannun hukumar bayar da agajin gaggawa da ke jihar Borno (SEMA). Tare da jaddada goyon bayan sa ga jama’ar karamar hukumar.
Kashim Shettima ya sake bayyana cewa ba don komai bane ya sa gwamnatin jihar Borno ta yanke shawarar raba wadannan kayan abinci tare da kayan tufafi ba, face domin ta rage wa jama’a yanayin radadin rayuwa, kana da yadda lokacin sanyin hunturu ke shigowa.
A hannu guda kuma, sanata mai wakiltar arewacin jihar Borno- Abubakar Kyari, a zauren majalisar dattawa, ya yaba da kaddamar da wadannan aikace-aikacen da Gwamnan ya yi a wannan yankin.
“gina sabbin gidaje har 500, babban abin a yaba ne, wanda idan ba a nan ba, ba a taba aiwatar da makamancin sa a ko’ina ba; a wajen birnin Maiduguri”. Inji shi.
Haka zalika kuma, tun daga bisani, shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Borno (SEMA), Yabawa Kolo, ya bayyana cewa wadannan motocin daukar kaya 16, wadanda aka makare su da kayan talkafin zuwa Gajiram, “fiye da rabin motocin sun kunshi kayan abinci ne da kayan masarufi somin a raba su kyauta ga yan gudun hijirar wannan yankin”.
A gefe guda kuma, daya daga wadanda suka ci gajiyar wannan tallafin, Modu Mustapha, ya bayyana farin cikin su dangane da wannan ci gaba da aka samu kuma abin a yaba.
“a matsayina na magidanci-mai iyali, kuma ina da yara guda hudu, wanda yanzu haka, an wayi gari bani da gidan da zan zauna- saboda yadda mayakan Boko Haram suka kona gidana kurmus”.
“Rayuwar mu ta kasance a cikin wannan matsugunin, wanda rayuwa ce mai dan-karen wahala matuka. Sannan baya ga bukatar gidaje, haka kuma muna fuskantar matsalar karancin ruwan sha”. Ya nanata.

Exit mobile version