Zubairu M Lawal" />

Gwamna Sule Ya Karyata Cewa Akwai Boko Haram A Nasarawa – Lai Muhammad

Ministan yada Labarai na kasa Alhaji Lai Muhammad ya bayyana wa manema labarai cewa Gwamna Abdullah Sule na jihar Nasarawa ya karya ta cewa akwai yan Kungiyar Boko Haram a Nasarawa.

Ya ce Gwamnan ya sheda masa cewa yan Jarida ne suka guzuri maganar amma ba haka ya shedawa Shugaban kasa Muhammad Buhari ba a ganawar da sukayi ranar jama’a 22/1/2021.
A ranar Littinin 25/1/2021 Minister yada labarai Alhaji Lai Muhammad ya shedawa manema labarai cewa Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya musanta cewa bai shedawa Shugaban kasa cewa akwai Membobin mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Nasarawa ba.
Babu labari mai kamar wannan a zantawarsa da shugaban kasa Muhammad Buhari a ranar jama’a.
A ranar jama’a Gwamnan ya ziyarce fadar Shugaban kasa a Abuja inda suka tattauna game da matsalar tsaro da ta addabi jihar Nasarawa.
Gwamnan ya sheda cewa bayan kama Membobin kungiyar Darulsalam 900 a jihar wadanda suka gudo daga jihar Nijer.. yanzu Membobin mayakan kungiyar Boko Haram sun kwararo zuwa jihar Nasarawa inda suke yaduwa dajin Toto da yayi iyaka da jihar Benue.
Gwamnan Sule ya nime taimakon Gwamnatin Tarayya domin kawar da miyagun yan Ta’adda dake shigowa jihar. Gwamnan ya tabbatar da matsalar tsaro a jihar Nasarawa.

Exit mobile version