Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi Allah-wadai da rikicin kabilancin da ya auku a kasuwar Sasha ta jihar Oyo, inda ya bayyana takaicinsa da cewa, wasu gungun matasa sun tsayar da zirga-zirgar jama’a a kan manyan hanyoyi, suna binciken fasinjoji don gano kabilarsu.
Ya ce, “na kasance koyaushe ina tattaunawa da takwarana na Jihar Oyo, Gwamna Seyi Makinde kan yadda za a dakatar da tashin hankalin,” in ji Gwamnan.
Gwamna Tambuwal ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fito daga fadar gwanatin jihar, inda yake cewa, “dukkanmu shaida ne game da zubar da jini wanda ya haifar da asarar rayuka da dama cikin awanni kadan da suka gabata bayan wani rikici da ya barke yayin da wani mai tura baro ya ture wata mata har ta ya sami mummunar rauni ta hanyar turewar, a kasuwar Sasha da ke Ibadan, jihar Oyo.”
Ya ci gaba da cewa, “Ba zato ba tsammani, rikicin zai iya rikidewa ya zama rikicin kabilanci tare da yiwuwar zubar jini saboda rashin jituwa idan har ba a hanzarta shiga tsakani ba.”
“A matsayinmu na kasa daya, dole ne mu nemi mafita cikin gaggawa game da wannan kisan gillar da muke yi wa junanmu yayin da ake ci gaba da kalubalantar rashin tsaro. Har ila yau, muna cikin matukar damuwa daga mummunar barnar da cutar korona da matsalolin tattalin arziki da matsin lamba suka yi mana, kuma muna da neman hanyar magance su don ganin cewa kyakkyawan shugabanci ya ci gaba. Don haka, ya saba wa hankali da daidaito ga wani rukuni na mutane don nuna wariyar launin fata ga ‘yan uwansu ‘yan kasa saboda kawai suna cikin wata kabila,” in ji Gwamanan.
Gwamnan ya ce, Don haka, mun ki, kuma mun yi Allah wadai da kyamar munanan al’amuran da suka mamaye al’ummomin Hausa da Yarbawa a karamar hukumar Akinyele ta Jihar Oyo.
Ya kara da cewa, “A yayin da muke yabawa Gwamna Makinde dangane da matakin da ya dauka na sanya dokar hana fitar dare zuwa karfe goma sha daya, da rufe kasuwar Shasha ba tare da baya cta lokaci ba, muna kira ga Gwamnatin tarayya da ta ci gaba da yawan ‘yan sanda a yankin tare da kara adadin jami’an tsaro da aka tsara a can.
“Haka kuma, dole ne dukkan hannaye su hau kan bene don tabbatar da cewa an yi amfani da zabin tattaunawa sosai yayin da ake kula da jin dadin wadanda abin ya shafa a cikin gajeren lokaci da kuma dogon lokaci.”