Gwamnan Jihar Zamfara, Honorabul Abdulaziz Yari, ya tababtar da cewa yau Alhamis Hukumar INEC, ta amshi jerin sunayen ‘yan takarar su na APC da babbar kotu ta uku ta Jihar Zamfara ta ba da umarnin amsar zaben fidda gwani da Jam’iyyar ta gabatar a ranar 3/10/2018. Sakamakon gamsuwa da shedun da aka gabatar a kotu na tabbatar da cewa, ‘Hukumar zabe mai zaman kanta ta amshi zaben fidda Gwani da jam’iyyar ta gabatar, kuma a yau Alhamis Jam’iyyar ta mikawa INEC, sunayen ‘yan takarar mu gabadaya. Muna gode ma Allah da samun wannna nasara.
Kuma ya yi kira ga Hukumar INEC da ta cika aikinta na amsar ‘sunayen ‘yan takarar daga Jam’iyya, Wanda shi ne babban aikinta. Idan akwai matsala tsakanin ‘yan takarar, sai kotu ta shiga tsakani ko da bayan zabe ne, idan takama a sake zaben ne sai a sake.
Kuma Gwamna Yari, ya tabbatar da cewa, ranar Litinin mai zuwa za su ci gaba da kamfen cikin fadin kananan hukumomin Jihar ta Zamfara.
Kusan wata uku kenan ana ta takaddamar kin amsar zaben fidda gwani da Jam’iyyar APC, ta Jihar Zamfara, ta gudanar a ranar 3/10/2018, wanda uwar Jam’iyyar ta kasa ta ce ta soke shi. Wanda a dalilin haka ne Shugabannin Jam’iyyar na Jihar Zamfara Suka kai kara kotu na cewa sun gudanar da zaben. Amma duk da haka, uwar Jam’iyyar ta ki amsar shi, sai ga shi yanzu kotu ta tabbatar da zaben.