Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a ranar Talata 4 ga watan Yuni, 2024 zai ayyana dokar ta baci kan ilimi a matsayin wani mataki na garanbawul a bangaren.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi, ya ce, yin hakan cika wani muhimmin alkawarin yakin neman zabe ne da ke kunshe a cikin shirin Gwamna Yusuf na 2022 mai taken “Alkawarina ga Kano.”
- Ƴansanda Sun Daƙile Yunƙurin Kai Hari Gidan Shugaban Jam’iyyar APC Na Kano
- Gobe Za a Tsunduma Yajin Aiki, An Gaza Cimma matsaya Tsakanin Gwamnati Da NLC
Tofa ya ce, sanarwar ta kuma yi daidai da shirin Gwamna na kara kaimi wajen inganta ayyukan ilimi da tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga daukacin mazauna yankin.
Gwamna Yusuf ya nuna matukar damuwarsa game da koma bayan ilimi a yankin, yana mai nuni da shirinsa na aiwatar da sauye-sauye a matakin manyan makarantu, sakandare da firamare.