Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Gwamna Zulum Ya Bude Cibiyoyin Kiwon Lafiya Biyar A Maiduguri 

by Muhammad
February 4, 2021
in LABARAI
1 min read
Gwamna Zulum
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Maitela,

Gwamnan jihar Borno, Prof. Babagana Umara Zulum ya bude cibiyoyin kiwon lafiya guda biyar a kwaryar birnin Maiduguri tare da kammala aikin gyaran babbar hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Bama, da sauran muhimman ayyuka, a ranar Laraba.

samndaads

Karin ayyukan da Gwamnan ya bude sun hada da cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko guda hudu da ke kan hanyar Baga, Njimtilo, rukunin gidaje 777 da a Abujan Talakawa, tare da asibitin cutuka masu saurin yaduwa da ke kan hanyar Kirikasamma.

Bugu da kari, Zulum ya bude aikin hanyar unguwar Abuja-Sheraton wanda daga bisani kuma ya dora harsashen ginin gina sabuwar asibiti mai gadaje 50 a unguwar Wulari duk a birnin Maiduguri.

Haka zalika kuma, Zulum ya shaidar da cewa, kafin hakan gwamnatinsa ta dauki daruruwan ma’aikatan kiwon lafiya a jihar domin ganin cibiyoyin sun gudana kamar yadda ya dace. Sannan kuma Gwamnan ya bayar da tabbacin sanya kayan aiki ga dukan cibiyoyin kiwon lafiyar da gwamnatin sa ta samar a kowane bangaren jihar hadi da kwararrun ma’aikata.

Dangane da ginin hanyar Maiduguri zuwa Bama, Gwamna Zulum ya sanar da cewa gwamnatin jihar tana tattaunawa da Alhaji Aliko Dangote domin samun tallafi kara tsawon hanyar daga Bama zuwa Banki- da zaran aikin hanyar ya isa garin Bama. Haka kuma ya kara da cewa aikin hanyar zai taimaka wajen bunkasa rayuwar al’ummar yankin.

A katshe, Gwamna Zulum ya yaba da ingancin ayyukan da ya bude, wadanda ma’aikatar kiwon lafiya a jihar ta aiwatar tare da ma’aikayar sake farfado da yankunan da matsalar tsaro ta shafa a jihar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Jami’o’i Masu Zaman Kansu 20

Next Post

Nda-Isaiah Mutumin Kirki Ne, Inji Magajin Garin Nupe

RelatedPosts

Sarkin Musulmi

Fulani Ba ‘Yan Ta’adda Ba Ne –Sarkin Musulmi

by Muhammad
9 hours ago
0

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce...

Sulhu Da Masu Garkuwa: Gwamnatin Zamfara Ta Amso Mata Takwas Da ‘Ya’yansu

Sulhu Da Masu Garkuwa: Gwamnatin Zamfara Ta Amso Mata Takwas Da ‘Ya’yansu

by Sulaiman Ibrahim
14 hours ago
0

Daga Hussaini Yero, Gusau A shirin Gwamnatin Jihar Zamfara na...

Gwamnatin Zamfara Ta Amshi Tubabbun ’Yan Bindiga Uku

Gwamnatin Zamfara Ta Amshi Tubabbun ’Yan Bindiga Uku

by Sulaiman Ibrahim
14 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed, Matawallen...

Next Post
Garin Nupe

Nda-Isaiah Mutumin Kirki Ne, Inji Magajin Garin Nupe

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version