Gwamna Zulum Ya Bude Cibiyoyin Kiwon Lafiya Biyar A Maiduguri 

Gwamna Zulum

Daga Muhammad Maitela,

Gwamnan jihar Borno, Prof. Babagana Umara Zulum ya bude cibiyoyin kiwon lafiya guda biyar a kwaryar birnin Maiduguri tare da kammala aikin gyaran babbar hanyar da ta tashi daga Maiduguri zuwa Bama, da sauran muhimman ayyuka, a ranar Laraba.

Karin ayyukan da Gwamnan ya bude sun hada da cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko guda hudu da ke kan hanyar Baga, Njimtilo, rukunin gidaje 777 da a Abujan Talakawa, tare da asibitin cutuka masu saurin yaduwa da ke kan hanyar Kirikasamma.

Bugu da kari, Zulum ya bude aikin hanyar unguwar Abuja-Sheraton wanda daga bisani kuma ya dora harsashen ginin gina sabuwar asibiti mai gadaje 50 a unguwar Wulari duk a birnin Maiduguri.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa kudirin gwamnatinsa shi ne samar da akalla cibiyar kiwon lafiya a cikin kowace gunduma 312 a jihar Borno, daidai da yadda hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta tsara.

Haka zalika kuma, Zulum ya shaidar da cewa, kafin hakan gwamnatinsa ta dauki daruruwan ma’aikatan kiwon lafiya a jihar domin ganin cibiyoyin sun gudana kamar yadda ya dace. Sannan kuma Gwamnan ya bayar da tabbacin sanya kayan aiki ga dukan cibiyoyin kiwon lafiyar da gwamnatin sa ta samar a kowane bangaren jihar hadi da kwararrun ma’aikata.

Dangane da ginin hanyar Maiduguri zuwa Bama, Gwamna Zulum ya sanar da cewa gwamnatin jihar tana tattaunawa da Alhaji Aliko Dangote domin samun tallafi kara tsawon hanyar daga Bama zuwa Banki- da zaran aikin hanyar ya isa garin Bama. Haka kuma ya kara da cewa aikin hanyar zai taimaka wajen bunkasa rayuwar al’ummar yankin.

A katshe, Gwamna Zulum ya yaba da ingancin ayyukan da ya bude, wadanda ma’aikatar kiwon lafiya a jihar ta aiwatar tare da ma’aikayar sake farfado da yankunan da matsalar tsaro ta shafa a jihar.

Exit mobile version