Gwamna Zulum Ya Yi Wa Mutanen Gwoza Goma Ta Arziki 

Gwamnatin Zulum

Daga Muhammad Maitela,

A ci gaba da kokarin sa na ganin ya kyautata jin dadin jama’ar jihar Borno baki daya, Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ranar Lahadi ya yi wa al’ummar Gwoza goma ta arziki ta hanyar kaddamar da raba naira miliyan 80 tare da kayan abinci ga kimanin mata yan gudun hijira 16,000, wadanda su ka dawo garuruwan su- a kudancin jihar.

Zulum ya isa garin Gwoza Jummu’a wanda a ranar Asabar ya jagoranci raba wa kanana da matsakaitan yan kasuwa tallafin naira miliyan 150 hadi da tallafin kayan abinci ga magidanta 27,000 wadanda mafi yawansu yan gudun hijirar Boko Haram ne da suka dawo yankunan su.

Bugu da kari, a ranar Lahadi Gwamnan ya ci gaba da aikin bai wa jama’ar tallafi, wanda kimanin mata 16,000 su ka samu tallafin naira 5,000 kowacen su tare da kayan abinci.

Gwaman ya sanar da cewa, gwamnatin jihar ta ci gaba da tallafa wa al’ummar yankunan da matsalar tsaro ta shafa domin rage musu radadin wahalhalun da suka fuskanta ta dalikin rikicin Boko Haram.

Garin Gwoza ya sha fama da hare-haren Boko Haram tun a shekarar 2014 wanda har ya kasance shugaban mayakan Boko Haram Abubakar Shekau ya rike garin Gwoza a matsayin cibiyar da suke gudanar da ayyukan su, kafin daga bisani a 2015 sojojin Nijeriya su kwato ta.

Bugu da kari, a daidai wannan lokacin, mayakan Boko Haram sun rusa daruruwan gine-ginen gwamnati da na jama’a kafin daga baya gwamnatin jihar ta farfado da garin ta hanyar gina wuraren da maharan suka rusa da kokarin dawo da walwala da jin dadin al’ummar garin.

A gefe guda kuma, a garin Gwoza, Gwamna Zulum ya kuma sake nanata shelanta daukar matakin dakatar da dokar hana bangar siyasa a fadin jihar Borno.

Exit mobile version