Gwamnan Adamawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri, ya tsallake rijiya da baya a wani harin da ‘yan binga sukakai a Lokoja stadium dake jihar Kogi, lokacin da jam’iyyar PDP ke gaf da kammala zaven fidda gwani da asubahin ranar Laraba.
Rahotanni daga Lokoja stadium inda lamarin ya auku, sun tabbatar da cewa ‘yan awanni kafin kammala qirga quri’a da sanada wanda yayi nasara, kawai sai ga ‘yan bindiga sun shigo filin wasan da jam’iyyar ke gudanar da zaven.
“mun kammala kaxa quri’a, muna kan tantance quri’un, kawai mukaji ‘yan bindiga sun iso wajajen qarfe xaya da minti arba’in da biyar na safiyar laraba (1:45am), munajin harbe-harbe ta vangarori daban daban” inji ganau.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa a kwatunan zaven takwas daga cikin goma an rigada an kammala qirgasu da tantancesu kafin zuwan ‘yan bindigar filin gudanar da zaven.
Anan take dai ‘yan takara, masu kaxa quri’u kowa yayi ta ransa domin neman tsira, kawo lokacin haxa wannan rahoton ba’akaiga tantance mutanen da suka jikkata ko rasa rayuka ba.
Dama dai gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, yana filin zaven ne a matsayin shugaban kwamitin gudanar da zaven, da shima ya tsallake rijiya ta baya daga harin ‘yan bindigar.

Exit mobile version