Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home Tambarin Dimukradiyya

Gwamnan Bauchi Amintaccen Dan Siyasa Ne, In Ji Jonathan

by Sulaiman Ibrahim
April 8, 2021
in Tambarin Dimukradiyya
3 min read
Gwamnan Bauchi Amintaccen Dan Siyasa Ne, In Ji Jonathan
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Tsohon Shugaban Nijeriya, Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya shaida cewar ana matukar wuyan samun ‘yan siyasan da za su rike amana wa mutum dari bisa dari bayan ya sauka a kujerar mulki.
Yana mai cewa a yanayin da ake akwai, da zarar mutum ya sauka daga kujerar mulki da daman ‘yan siyasa sulalewa suke yi daga jikinsa su daina masa biyayya balle ma har su tuna da shi a matsayin wani jigon da ya kyautata musu a lokacin da yake bisa karaga.
Sai dai Jonathan ya ce a irin wannan yanayin ya amince ya kuma gamsu da cewa Sanata Bala Muhammad amintaccensa ne kuma dan siyasa ne wanda ya rike amanarsu har bayan da ya sauka daga kan mukamin shugaban kasa, ya nuna hakan a matsayin abun yabo da jinjina matuka gaya.
Ebele wanda ke wannan bayanin a Bauchi yayin da ke kaddamar da sabun titi mai nisan kilomita 6.25Km da ya tashi daga Sabon Kaura zuwa kan babban hanyar Jos by-pass da ke daidai yankin Miri wanda gwamnatin Bala Muhammad ta gina.
“Akwai wasu mutanen da za ka gansu kamar ba za su iya cin amanarka ba lokacin da kake kan mulki. Amma da zarar ka sauka ko ka bar kan wannan mukamin, za su sulale su barka kamar ba su taba rayuwar amana da kai ba.
“Yau ta kasance babban rana na farin ciki sosai a gare ni, kun san meye sa? Saboda ba karamin lamari ba ne ka samu mutumin da ya yi aiki da kai a Nijeriya kuma bayan ka bar ofishinka, wannan mutumin ya cigaba da rike maka wannan kyakkyawar alakar da ke tsakaninku.
“Na kasance a cikin lamarin shugabanci na tsawon lokaci da na hau kan mukamai daban-daban da na fara tun daga kan mataimakin gwamna.
“Abun da na yi masa fahimta sosai shine bayan ka fita daga ofis wasu mutane za su mance da kai kamar ba su taba rayuwa tare da kai ba.
“Amma, Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi dan uwa ne na kwarai don haka cike nake da murna da ya gayyaceni domin kaddamar da fara amfani da babban aiki na farko da ya aiwatar, wannan karamci ne sosai a gareni.”
Tsohon shugaban kasar ya nuna godiyarsa ga al’umman Jihar Bauchi a bisa zabin da suka yi wa Bala Muhammad a matsayin gwamnan jihar, yana mai bada tabbacin cewa tabbas yana da kwarin guiwar Bala zai cigaba da gudanar da nagartattun ayyukan raya jihar da bunkasata.
Jonathan sai ya yaba da irin ayyukan raya jihar da Bala ke gudanarwa, ya horesa da ya cigaba da yin hakan domin kyautata jihar da ma kasa baki daya.
Tun da farko, gwamna Bala Muhammad, ya bayyana cewar wannan aikin na daya daga cikin muhimman ayyukan da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa a farkon kwanakinta 100 a bisa mulki.
Bala ya ce, ya bada aikin ne a kan kudi naira biliyan 2.2 wa kamfanin Habib Engineering Limited da suka samu nasarar farawa da kammala aikin cikin watanni shida kacal.
“Mun himmatu wajen gudanar da nagartaccen shugabanci da zai bada damar kafa tarihin aiwatar da dumbin ayyukan raya jihar domin bada damar kyautatawa da inganta rayuwar al’umman Jihar Bauchi.
“Ya mai girma, ka sani sarai, ban san wannan al’adar ba, kai ne ka koya min lokacin da nake cikin mukarrabanka.”
Bala yana mai cewa zuwa yanzu, gwamnatinsa ta samu nasarar gudanar da ayyukan shimfida hanyoyi na sama da kilomita 100 a sassan birane da karkaran jihar.
Ya kuma ce, sun rangada wa babban hanyar Sabon Kaura zuwa Miri ne ga sunan Goodluck Jonathan domin ake tunawa da irin kyakkyawan shugabancin da ya yi wa kasar nan.

SendShareTweetShare
Previous Post

2023: Gwamnonin Da Suka Sha Alwashin Mara Wa Tinubu

Next Post

Fasahar Sadarwar Zamani Za Ta Bunkasa Sauyin Tattalin Arziki – Shugaba Buhari

RelatedPosts

LSO Ta Fara Wayar Da Kan Jama’a Muhimmancin Mallakar Katin Zabe

LSO Ta Fara Wayar Da Kan Jama’a Muhimmancin Mallakar Katin Zabe

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna kungiyar Magoya Bayan Hon. Abubakar...

Rikicin Shugabanci: An Yi Hadin Baki Da ‘Yan APC Ne Domin Rusa PDP – Abubakar Kadawa

Rikicin Shugabanci: An Yi Hadin Baki Da ‘Yan APC Ne Domin Rusa PDP – Abubakar Kadawa

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano An bayyana cewa dan hargitsin...

APC

Gurbatattun ‘Yan Siyasa Ke Haddasa Rashin Tsaro Da Kabilanci A Nijeriya – Jigon Jam’iyyar APC

by Sulaiman Ibrahim
1 day ago
0

Wani jigon jam’iyyar APC ya bayyana cewa, ba za a...

Next Post
“Duk Da An Sauya Shugabannin Tsaro, Har Yanzu Da Saura”

Fasahar Sadarwar Zamani Za Ta Bunkasa Sauyin Tattalin Arziki – Shugaba Buhari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version