Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sayo rigakafin cutar Korona lura da cewa wadanda wasu hadakar kungiyoyi suka baiwa kasar nan kyauta ba za su wadaci dukkanin ‘yan kasar nan ba.
Bala, wanda ya lura da cewa adadin rigakafin da aka kawo cikin Nijeriya ya kasa idan aka yi nazarin miliyoyin al’umman da ke rayuwa a cikin kasar, yana mai cewa ya kamata adadin da Nijeriya za ta samu ya zarce na jamhuriyyar Nijar, Kamaru da Chadi a cewarsa Nijeriya ta fi su yawan al’umma.
Kan haka ne ya jinjina wa kungiyoyin da suka baiwa Nijeriya tallafin rigakafin korona, yana mai cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya da ta jihohi da su hada hannu waje daya domin sayo karin rigakafin korona da zai wadatar da dukkanin ‘yan kasar nan.
Bala Muhammad yana wannan bukatar ne a jiya jim kadan bayan da aka yi masa rigakafin cutar Korona tare da mai dakinsa, Aisha Bala Muhammad, hade da masu ruwa da tsaki da suka kunshi jami’an gwamnati, ‘yan siyasa, ma’aikata, da sauransu, a gidan gwamnatin jihar yayin kaddamar da fara rigakafin ta Korona a jihar.
Gwamna Muhammad ya nuna cewa rigakafin na korona na da matukar amfani wanda ya kore dukkanin wata jita-jitan da ake yadawa kan rigakafin, yana mai cewa babu wani illa ko aibu da rigakafin ke da shi, a bisa haka ne ma ya nemi jama’an jihar da su rungumi rigakafin hannu biyu-biyu.
Yana mai kuma karawa da cewa da zarar jama’a suka yi rigakafin, su samu cikakken kariya daga cutar Korona wacce ta illata da kashe dubban jama’a a fadin duniyar nan ‘yan watannin baya.
A gefe daya, gwamnan ya nuna jin dadinsa kan yadda malamai da fastoci suka bayyana tare da amsar rigakafin a lokacin da aka kaddamar, yana mai cewa hakan na nuna cewa ba za a samu wata matsala wajen amsar rigakafin ba a jiharsa, har ma ya ce akwai kyakkyawar fatan jama’a za su yi koyi da malamai, limamai, fastoci da sauransu wajen ganin su ma sun amince an musu rigakafin.
Bala, ya kuma ce adadin dozin sama da dubu 150 da aka ware wa jihar Bauchi ya kasa, kuma sauran jihohi ma yana da yakinin adadin da aka ba su ba zai wadaci al’ummominsu ba, don haka ya ce tabbas akwai bukatar cire kudade domin sayo rigakafin ba sai an jira na kyauta ba.
“Lafiyar al’umma na gaba da komai don haka ina kira ga gwamnati tarayya da ta sayo karin rigakafin korona domin kula da lafiyar al’umma Nijeriya. Ya dace gwamnatin tarayya da mu gwamnoni mu hadu domin sayo karin rigakafin nan.”
“Mun zo nan domin a mana rigakafin korona a matsayinmu na shugabanni domin mu nuna cewa tabbas fa rigakafin nan bai da wani illa don haka muke fada wa al’ummanmu da su amince a musu rigakfin nan, yin zai baiwa mutum tabbacin kariya daga cutar.”
Bala yana mai gode wa kungiyoyin abokan jere na kasa da kasa musamman hukumar lafiya ta duniya WHO a bisa sadaukarwa da jajircewa waje kare rayukan ‘yan Nijeriya, sai ya nemi karin hadin kai a tsakanin kungiyoyin da gwamnati domin kara tsarkake Nijeriya daga cutuka masu yaduwa.
Sannan, ya jinjina tare da yaba wa kwamitin yaki da cutar Korona a karkashin mataimakin gwamnan jihar Sanata Baba Tela bisa himma da kwazonsu wajen tabbatar da kare al’umma jihar daga wannan mummunar annobar ta korona tun lokacin da ta barke a jihar.
Shi ma a jawabinsa, shugaban kwamitin yaki da Korona a jihar, Sanata Baba Tela ya bayyana cewar jihar ta samu dozin-dozin 80,570 na rigakafin Korona daga cikin adadin dozin 150,000 da hukumar lafiya a matakin farko ta tarayya (NPHCDA) ta ware wa jihar a kokarinsu na tabbatar da kare jama’a daga kamuwa da cutar na Korona.
Ya ce wannan rigakafi ne wanda aka tantance kuma kasashen duniya da dama su na amfani da shi, yana mai neman jama’a da su amshi rigakafin da zuciya daya.
Ya kara da cewa za a kai rigakafin dukkanin kananan hukumomin da suke jihar 20 da gundumomi 323 domin yi wa jama’a rigakafin a sauwake.
Ya nemi jama’a da su rungumi rigakafin ba tare da wani taraddidi ba domin ya bada tabbacin cewa Gwamnatin jihar a kowani lokaci muradinta shine kare rayuka da dukiyar jama’a gami da lafiyarsu.
Tun da farko, kwamishinan lafiya na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Maigoro, ya shaida cewar tunin suka samar da jami’an lafiyan da za su yi aikin rigakafin a kowani yanki na jihar, kuma tunin aka yi wa jami’an lafiyar nasu rigakafin domin su kasance sun yi rigakafin kafin su yi wa sauran jama’a.
Yana mai cewa rigakafin na da matukar amfani domin kare al’umma daga annobar ta Korona.
Ya ce za su yi allurar rigakafin ne daidai da tsari da ka’idar da aka gindaya musu.