Khalid Idris Doya" />

Gwamnan Bauchi Ya Gargadi Sarakunan Jihar Kan Mara Wa Ta’addanci Baya

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya gargadi Sarakunan jihar dangane da mara wa aikace-aikacen ta’addanci baya a yankunan masarautunsu.

Gwamnan wanda ya yi gargadin a lokacin da ya amshi bakuncin majalisar sarakuna ta jihar a karkashin shugabansu, Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu a gidan gwamnatin jihar a cikin makon nan.

Gwamna Bala ya shaida cewar gwamnatinsa ba za ta taba lamuntar aiyukan ta’addanci ba, don haka ne ya nemi masu rike da sarautun gargajiyan da suke kokarin daukar matakan magance matsalolin tsaro da suke yankunansu da kuma kauce wa yin dukkanin abun da zai zama mafaka ko kariya ga masu aikata ta’addanci domin tsarkake jihar daga masu mugun aiyuka.

Gwamnan ya bayyana cewar wasu yankunan da suke jihar suna fama da ‘yan garkuwa da mutane da fashi da makami, don haka ne ya nemi goyon bayan masu rike da sarautun gargajiyan wajen shawo kan matsalar da kuma tabbatar da tsaro da kare rayukan jama’a.

Baya ga gargadin Gwamnan ya kuma rokesu da su tabbatar da sun yi dukkanin mai iyuwa wajen tabbatar da tsaro da kare rayukan jama’a ya samu tagomashi a jihar.

Jagoran sarakunan, Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman Adamu ya bayyana cewar sun kawo ziyaraar ne domin taya gwamnan murnar samun nasara a kotun sauraron kararrakin zabe, gami kuma da bashi tabbacin goyon bayansu wurin samun nasarar gwamnatinsa.

Dakta Rilwanu ya yi amfani da damar wajen yaba wa nasarori da gwamnan ya samu cimmawa a dan zangonsa da ya yi a matsayin gwamna kama daga harkar ilimi, lafiya, ilimi, tsaro, samar da aiyukan hanyoyi da kuma samar wa mata da matasa ababen dogaro da kai da ya himmatu wajen yi a dan watannin da ya shafe a matsayin gwamnan jihar.

Exit mobile version