Gwamnan Bauchi Ya Isa Kasar Amurka Don Tattauna Yadda Za A Inganta Zaman Lafiya A Jiharsa

PIC. 20. GOVERNOR-ELECT FOR BAUCHI STATE, ALHAJI MOHAMMED ABUBAKAR (L) AND INCUMBENT GOV. ISA YUGUDA, DURING THE TRANSITION MEETING AT RAMAT HOUSE IN BAUCHI ON WEDNESDAY (15/4/15). 2013/15/4/2015/DJ/BJO/CH/NAN

A ranar Juma’a 30/3/2018 ne Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya tafi kasar Amurka domin ganawa ta musamman da Sakataren majalisar dinkin duniya kan zaman lafiya da shawo, domin ganin yadda za a samar da zaman lafiya mai daurewa a jihar.

Ziyarar wacce za a ta bayar da dama a tattauna ta musamman kan yadda za a samu inganta zaman lafiya a jihar ta Bauchi, bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da fadar gwamnatin jihar Bauchi ta raba wa manema labaru a ranar 30/3/2018 dauke da sanya hanun babban mai baiwa gwamnan jihar shawarori kan harkokin yada labarai da kuma tsare-tsare wato Ali M Ali.

Sanarwar ta kara da cewa “ziyarar za ta kawo wa sha’anin zaman lafiya ci gaba a jihar Bauchi, shiyyar Arewa Maso Gabas da ma kasar baki daya, domin tattauna yadda za a kawo karshen tabarbarewar matsalolon tsaro da suka addabi wasu yankuna tun shekarun baya,” A cewar Ali M.

Ali Muhammad Ali ya ce ziyarar za ta yi dubiyar yadda za a samu zamar lafiya mai daurewa da kuma hanyoyin da za a bi domin shawo kan matsalolin.

Baya ga haka kuma, gwamnan zai tattauna kan wasu muhimman batutuwa da za su kawo wa jiharsa ci gaba mai ma’ana.

Ali M. Ali ya ce ana sa ran gwamnan jihar ta Bauchi Muhammad Abubakar zai dawo gida jihar Bauchi ne a ranar 6 ga watan Afrirul 2018 bayan kammala ziyarar tasa a kasar ta Amurka.

Wadanda suka mara masa baya zuwa wannan ziyarar tattauna yadda za a samu habaka zaman lafiya sun hada da babban mai tsatsara lamura (SCOP), Sulaiman Malami, Babayo Liman, da babban tallafa wa kan harkar zaman lafiyan, Yazid Inuwa da kuma sauran wadanda abin ya shafa.

 

Exit mobile version