Khalid Idris Doya" />

Gwamnan Bauchi Ya Kaddamar Da Rabon Adaidaita 345

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya kaddamar da rabon rancen Keke-Napep guda dari uku da arba’in da biyar (345) ga masu sana’ar kabu-kabu domin karfafa musu kwiwa kan sana’o’insu tare da bunkasa tattalin arzikin jihar.

An raba musu Mashina masu kafa ukun ne da zimmar su biya kudinsu cikin shekaru biyu masu zuwa domin sake juya kudaden don wasu ma su amfana. Samar da bashin Keke-Napep din na zuwa ne a sakamakon haramta sana’ar Achaba da gwamnan jihar ya yi a kwanakin baya domin kare al’umman jihar daga annobar Korona.

A lokacin da yake jawabi a yayin bikin da ya gudana a jiya, Gwamna Bala Muhammad ya shaida cewar sun samar da wannan tsarin ne domin taimaka wa jama’a musamman matasa tare da fitar da su daga cikin kunci na talauci, yana mai cewa tunin gwamnatinsa ta ware naira miliyan 250 domin tabbatar da shirin ya samu kankama.

Kamar yanda yake cewa, kashi na farko kenan na rabon wanda ya ce da zarar wadanda suka ci gajiyar rabon na farko suka maido da kudaden za a sake amfani da su wajen sake sayo wasu Kekunan domin wasu ma su amfana.

“Idan za ku iya tunawa, gwamnati ta haramta sana’ar Achaba a jihar nan domin tsaro da kuma dalilai da suka shafi na lafiya. A bisa yunkuri gwamnati na samar da mafita, Gwamnatin jihar ta dauki matsayar samar da Keke-napep guda 1,000 da za su sauya sana’ar Achaba da aka hana,” A cewar shi.

Gwamnan ya jawo hankalin wadanda suka samu nasarar samun ababen hawan da su tabbatar da sun mutunta dokokin da aka shimfida domin samun nasarar kyautatuwar tattalin arzikinsu hadi da na jihar gami kuma da sauwake wa jama’a wahalhalun sufuri.

Ya na mai shan alwashin samar da ababen hawan za su yi matukar taimakawa ta fuskacin bunkasa sufuri da zirga-zirga a jihar.

A gefe daya, gwamnan ya sha alwashin cewar nan gaba kadan Gwamnatin jihar za ta sayo wasu karin motocin kabu-kabu domin bunkasa wa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwan da suke sana’ar kabu-kabu tattalin arzikinsu.

Tun da farko, Kwamishinan kanana da matsakaitan sana’o’i ta jihar,  Alhaji Usman Saleh, ya shaida cewar an tsara a kowace rana duk wanda ya samu Keke-napep din zai ke biyan naira dubu daya kana zai biya kudin Keke-napep din ne a cikin shekaru biyu kacal daga bisani ya mallaki abun hawar.

Ya kuma ce, gwamnan jihar ya janye dukkanin wani takurawa ko karin wasu kaso ga masu cin gajiyar domin tabbatar da sun mori ababen hawan yanda ya dace ba tare da takuri ba. Ya kuma ce an yi tsare-tsare na musamman da kowa zai ji dadin lamarin ba tare da takuri ba.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewar sauran Keke-napep din Gwamnatin ta sayo su nan da karshen shekarar nan da muke ciki.

 

Exit mobile version