Gwamnan Bauchi Ya Nada Aminu Gamawa A Matsayin Shugaban Ma’aikata

Daga Khalid Idris Doya

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya nada Dakta Aminu Hassan Gamawa a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin jihar (CoS).

A wata sanarwar da aka wayi gari da ita daga fadar jihar dauke da sanya hannun babban mashawarci na musamman wa gwamnan kan yada labarai da hulda da ‘yan jarida, Kwamared Mukhtar Gidado, ta nuna cewa wannan nadin nan take ne ta fara aiki bisa amincewar gwamnan.

Kafin wannan nadin, Gamawa shine Kwamishinan kasafin da tsare-tsaren tattalin arziki wanda gwamnan ya rushe su tare da sauran Kwamishinoni, sannan, ya maye gurbin Ladan Salihu da gwamnan ya tsube daga wannan mukamin na CoS ‘yan kwanaki kalilan da yin hakan.

A saanrwar ta Gidado, ya bayyana cewa Aminu Gamawa ya samu shaidar karatun digiri na biyu da na uku ne a fannin koyon ilimin Shari’a a makarantar Harvard Law School da ke jami’ar Harvard a kasar Amurka.

“Haifafen dan karamar hukumar Gamawa ta jihar Bauchi ne. Kwararren masanin Shari’a, Malami, kuma hazikin ma’aikacin gwamnati. Ya yi aiki a ciki da waje da kungiyoyi daban-daban da rassan gwamnati da dama, cibiyoyin ilimi da wasu rassan ma’aikatu masu zaman kansu.”

Exit mobile version