Gwamnan Bauchi Ya Rantsar Da Shugabannin Kananan Hukumomi

gwamnan bauchi

Daga Khalid Idris Doya

 

A jiya Lahadi ne gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya rantsar da sabbin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar su 20, tare da kiransu da su jawo al’ummansu a jika domin kyautata mulki a kowani lokaci, kana su yaki cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikatan da suke kananan hukumomin su.

Gwamnan wanda ya ba su shawaran hakan a lokacin da ke rantsar da su a gidan Gwamnatin jihar, ya ce muddin suka yi aiki kafada da kafada da al’ummominsu tun daga tushe hakan zai bada dama su samu cimma muradun da jama’a suke fata a kansu.

Gwamnan Bala ya fa tunashesu da cewa shekaru biyu da suke da su a matsayin zababbun su yi amfani da damar wajen kyautata mulki da kokarin samar da ci-gaba domin farfado da kananan hukumomin su, ya nemesu da cewa duk abun da za su yi, su himmatu don baiwa marar da kunya.

Ya kuma jawo hankalinsu da su kasance masu ririta dukiyar kananan hukumomin su ba tare da almubazzaranci ba, inda a cewarsa dukkanin ayyukan da za su aiwatar su yi kokarin sanya lura matuka domin bunkasa rayuwar wadanda suka zabesu.

Gwamna Bala Muhammad sai ya nemi Shugabannin da su dafa wa kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da dakile ma’aikatan bogi da suke hana jihar zakudawa gaba, inda ya ce su tabbatar da sanya ido sosai kan ma’aikatan da suke yankunan su domin cire baragurbi daga ciki don ba su damar samun kudaden gudanar da ayyukan da za su taimaka ma wadanda suka zabesu.

Daga bisani ya nuna matukar farin cikinsa bisa samun nasarar gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali, ya taya su murna a bisa lashe zabukansu da suka yi tare da ba su tabbacin goyon baya domin su samu damar cimma manufofin kyautata yankunansu.

“Shekaru 12 ba tare da gudanar da zaben Kananan Hukumomi a jihar Bauchi ba, don haka abun murna ne sosai da muka samu zarafin yin zaben nan a wannan lokacin. Ina gode wa Allah da ya baiwa gwamnatinmu damar yin zaben nan wanda yana daga cikin alkawuran da muka yi a lokacin yakin neman zabe. Allah kuma cikin yardarsa ya baiwa jam’iyyar PDP nasara lashe zabukan,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma bukaci zababbun da su tabbatar da maida hankali kan lamuran tsaro domin tabbatar da kare rayuka da dukiyar al’ummominsu.

Wakilinmu ya labarto cewa jam’iyyar PDP ce ya lashe dukkanin zabukan kananan hukumomin 20 da na kansiloli 323 da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata. Inda jam’iyyun siyasa guda 18 suka shiga aka fafata da su.

Da ya ke mika wa zababbun shaidar cin zaben da safiyar jiya Lahadi, shugaban hukumar Alhaji Dahiru Tata ya taya zababbbun murnar lashe zaben, daga bisani ya mika wa kowa shaidar cin zabe.

Tata ya ce an gudanar da zaben ne a karkashin sanya idon jami’an tsaro, yana mai cewa an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Zababbben Shugaban karamar hukumar Bauchi Mahmud Baba Ma’aji ya nuna farin cikinsa a bisa wannan matakin, yana mai cewa shi da sauran zababbu za su yi dukkanin mai yiyuwa wajen tabbatar da sauke nauyin da aka daura musu.

Ya nemi wadanda suka fafata neman sa’a da su da cewa su daure su zo su hada karfi da karfe domin ciyar da jihar Bauchi gaba.

Shi ma Shugaban karamar hukumar Bogoro Iliya Habila ya sha alwashin kyautata mulki a karamar hukumarsa tare da nuna cewa zabin nasu zai yi matukar baiwa kananan hukumomin jihar zarafin samun ababan more rayuwa kai tsaye.

An dai samu karancin masu fito kada kuri’a a yayin zaben inda jama’a da dama ba su bi dokokin hana cinkoso don kariya daga Korona ba kamar yadda Wakilinmu ya nakalto, sannan an samu korafe-korafen rashin zuwan kayan zaben a kan lokaci daga sassa daban-daban na rumfunan zaben.

Zababbun shugabin sun hada da: Karamar hukumar Bauchi Mahmoud Baba Ma’aji; Alkaleri Yusuf Garba; Bogoro Iliya Habila; Damam Waziri Ayuba; Darazo Mahmood Bello; Dass Bello Haruna; Gamawa Yaya Hamma; Ganjuwa Daiyabu Mohammad Kariya; Giade Usman Mohd Sale; Itas/Gadau Abdullahi Mohd Maigari; Jama’are Sama’ila Yusuf Jarma.

Sauran sune: Katagum Abdullahi Kuda; Kirfi Garba Musa; Misau Abubakar Ahmed Misau; Ningi Ibrahim Zubairu; Shira Babangida Ishak Abdullahi; T/Balewa Daniel Mazadu Danjuma; Toro Adamu Umar Danyaro; Warji Adamu Muhammad; Warji Zaki Yahuda Abdulkadir.

 

Exit mobile version