Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnan Bauchi Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Alkinta Haraji Wuri Guda

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya sanya hannu kan dokar daidaitawa, tattarawa da kuma alkinta dukkanin kudaden shigar jihar na ma’aikatu, sassa, hukumomi na jiha da na kananan hukumomin Bauchi da sauran dalilan da su ke da alaka da wannan dokar.

Sanya hannu kan dokar da ya gudana a jiya a gidan gwamnatin jihar a inda gwamnan ke bada yakin cewa za su tabbatar dokar ta yi aiki gadan-gadan domin tabbatar da tattarowa tare da adana kudaden shiga ga sahihin hanya.

Gwamnan ya yi bayanin cewa, dokar za ta kyautata tare da inganta hanyoyin shigar kudi tare kuma da toshe kafofin handame dukiyar haraji.

Ya na mai cewa, gwamnatin jihar ta fito da tsare-tsaren da suke kan doka da oda da za su kyautata gudanar da gwamnati, tare da kyautata hanyoyin tattara kudaden shiga cikin sauki da ‘yan kasuwa za su biya ba tare da jin radadin hakan biyan ba.

Ya na mai cewa kudurin sai da ya je gaban majalisar dokokin jihar gabanin su amince da shi tare da zamar da shi bisa doka.

Ya na mai cewa tsarin da suka tahowa da shi zai inganta tare da samar da damarmakin toshe kafofin rashawa tare da dakile karkatar da dukiyar al’umman jihar.

“Mun bi da lamarin ta hanyoyin doka sannan mun yi amfani da tsarin zamani na kimiyya masu nagarta da za su tabbatar da kudaden shigarmu suna tafiya daidai da zamani tare da kaiwa ga matakin da babban bankin duniya ta gindaya domin rage dogaro kacokam daga lalitar gwamnatin tarayya.”

Gwamna Bala Muhammad ya kuma shaida kudurin da ya sanya hannu a kai din, zai kyautata sashin shigar kudi da zai bada dama a aiwatar da kyawawan aiyukan raya jiha da al’umman jihar.

Tun da farko, Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Y Suleiman, ya shaida cewar majalisar ta bi dukkanin matakan da suka dace wajen amincewa da kuduri.

Ya nemi gwamnan jihar da yayi aikin hadaka da ‘yan majalisar domin kyautata rayuwar al’umma. Daga nan sai ya jinjina a bisa hadin kai da ake samu a tsakanin majalisar da gwamnatin jihar wanda ya misalta hakan a matsayin hanya ta cigaban jihar Bauchi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: