Gwamnan Bauchi Ya Rushe Majalisar Zartaswar Jihar

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Bauchi Sanata Bala Muhammad ya rushe dukkanin mambobin Majalisar zartaswar jihar kama daga Kwamishinoni, Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati (COS) da dukkanin masu mukaman siyasa.

A wata sanarwa da babban mai ba shi shawara kan yada labarai da hulda da ‘yan jarida, Kwamared Mukhtar Gidado ya fitar a safiyar nan na cewa gwamnan ya amince da sallamar dukkanin Kwamishinoni da sauran mukaman siyasa ciki har da manyan jami’an Gwamnati wato SSG da COS.

Ya ce mukaman da wannan rushewar bai shafa ba kawai su ne Babban Mai bada shawara Kan harkokin tsaro; Babban Mai bada shawara kan harkokin Majalisun tarayya da ta jihar; Babban Mai bada shawara Kan zuba hannun jari da kuma Babban Mai bada shawara Kan yada labarai da Hulda da ‘yan jarida.

“Dukkanin Kwamishinoni an umarce su da su mika ragamar ma’aikatunsu ga manyan sakatarorin dindindin na ma’aikatunsu.

“Sannan Sakataren Gwamnatin jihar da Shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati da sauran mukaman siyasa su kuma su mika ragamar ma’aikatunsu ga Babban Sakataren da ya fi kowani Sakataren girma a fannin aiki.”

Sanarwar ta nemi da su ajiye dukkanin kadararorin gwamnati da suka sani na hannunsu kafin barinsu ofis, indai sanarwar ya ce nan take ne wannan rushewar ta fara aiki.

Daga bisani gwamnan ya gode musu a bisa ba shi gudunmawa wajen ciyar da jihar Bauchi gaba da suka yi a lokacin da suke bakunan aikinsu tare da musu fatan alkairi a rayuwarsu na gaba.

Exit mobile version