Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnan Bauchi Ya Sa Hannu Kan Sabon Kasafin 2020 Na Biliyan N129

Published

on

  • Jihar Ta Rada Wa Makarantu Sunan Belinda & Gates Da Dangote

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya sanya hannu kan sabon kasafin kudi na 2020 da cutar Korona ta tilasta wa jihar rage hawan kudin zuwa biliyan 129 a maimakon biliyan 167 da aka yi harsashe a kasafin tun da farko.
Baya ga wannan, gwamnan ya kuma sanya hannu kan dokokin da suka shafi keta haddin bil-adama, canza wa kwalejin lafiya ta ‘College of Health Technology Ningi’ suna zuwa ‘Belinda and Gates College of Health Technology Ningi’, tare da sauya wa kwalejin koyar da nas-nas da ingozoma ‘College of Nursing and Midwifery’ suna zuwa Aliko Dangote.
Sauran dokokin da gwamnan ya sanya musu hannu domin su zama doka sun hada da kafa Bauchi State Public Procurement 2020 tare da sauya suna wa kwalejin AD Rufai College of Legal studies zuwa AD Rufai College of Education and Legal Studies.
Da ya ke jawabi bayan sanya hannu kan sabbin dokokin, gwamna Bala Muhammad, ya shaida cewar gwamnatinsa na aiki kafada da kafada da majalisar dokokin jihar domin tabbatar da yin aiki tare da zai kai ga samar da kyakkyawar shugabanci.
A cewarsa sake nazarin kasafin kudin 2020 tare da zaftareshi ya faru ne a sakamakon tasirin da annobar Korona ta yi wa tattalin arzikin jihar, kasa da ma duniya baki daya.
A cewar shi har zuwa yanzu dai sabon kasafin ya fi bada fifiko da muhimmanci ga sashin lafiya, ilimi, noma da kuma gudanar da aiyukan raya birani da gina al’umma, yana mai lura da cewa, gwamnatin jihar ta yi tsare-tsare masu kyawu domin tabbatar da dukkanin aiyukan da aka tsara an samu aiwatar da su domin gina wa al’umman jihar rayuwarsu.
A cewar shi, hadin kai da majalisar dokokin jihar take ba shi abun yabawa ne, yana mai basu tabbacin zai ci gaba da nasa kokarin domin yin aikin da zai kyautata rayuwar talakawa.
Gwamna Bala yana cewa tun kafin ma zuwan annobar Korona tunin gwamnatinsa ta samu kammala wasu daga cikin aiyukan da ta tsara gudanarwa.
Dangane da kwalejojin lafiya guda biyu da jihar ta sauya musu suna, gwamnan ya bayyana cewar yin hakan ya zama dole domin nuna karamci da sakayya a bisa na mijin kokarin da jigogin da aka sanya sunansu suke bada wa wajen samun nasarar ingantuwar kiwon lafiya.
A jawabinsa, Kakakin majalisar Dokokin jihar Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Y Suleiman, ya misalta dokokin a matsayin muhimman da za su kai ga inganta jihar Bauchi.
Ya kuma bada tabbacin cewar za su ci gaba da baiwa gwamnatin jihar hadin kai domin tabbatar da kwalliya na biyan kudin sabulu.
Advertisement

labarai