Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Gwamnan Bauchi Ya Tallafa Wa Iyalan Wadanda Suka Rasa Rayukansu A Kifewar Kwale-kwale

by Khalid Idris Doya
January 30, 2021
in LABARAI
2 min read
Kiran Da Tsohon Gwamna Shema Na A Dawo Tafiyar PDP Ya Makara –inji PDP A Gyara
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Iyalan mutum 11 da suka rasa rayukansu sakamakon kifewar kwale-kwale a kogin Buji da Garin Dole da ke karamar hukumar Itas Gadau a kwanakin baya sun samu tallafin naira miliyan biyu daga hannun Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad domin rage musu radadi.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Abdullahi Maigari, shine ya shaida hakan a yayin rabon kudaden ga iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon wannan iftila’in.

samndaads

Maigari wanda ya shaida cewar kowani mutum daga cikinsu zai samu naira dubu dari (N100,000) na rage radadin halin da suka tsinci kai a ciki, ya kara da cewa al’ummomin da suka samu tallafin su sani ba wai diyyar asarar da suka yi ne aka biya su ba; a’a kawai tallafin rage radadi ne gwamnan ya ba su, sai shawarcesu da su dauki lamarin da ya faru a matsayin mukaddari daga Allah.

A cewarsa cikin kwanaki dari da ya yin a farko a matsayinsa na zabebben shugaban karamar hukumar, an samu aiwatar da muhimman ayyukan da suka dace wajen ganin an inganta rayuwar jama’a da suka kunshi, sashin wutar lantarki, ruwa mai tsafta, lafiya, ilimi, tallafa wa kungiyoyi, da agazawa kungiyoyin addinai tare da ‘yan kasuwa domin rayuwa take ingantuwa.

Idan za ku iya tunawa dai, jama’a 18 ciki har da iyaye mata ne suka rasa rayukansu sakamakon tsautsayin da ya faru na kifewar jirgin ruwa a cikin kogin Buji.

SendShareTweetShare
Previous Post

Rashin Iyan Bashir: Babban Gibi Ne In ji Ya Salaam

Next Post

Fadar Shugaban Kasa Ta Gargadi Masu Yunkurin Batanci Ga Buhari

RelatedPosts

Saura Wata Biyu Buhari Ya Dawo Da Zaman Lafiya –Sanata Lawan

by Khalid Idris Doya
5 hours ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad...

Sojoji Sun Sake Kwato Garin Marte A Borno

Sojoji Sun Sake Kwato Garin Marte A Borno

by Khalid Idris Doya
13 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim Sojojin Nijeriya a yammacin yau, da misalin...

Gwamnatin Bauchi Ta Raba Keke-Napep 1,000 Don Bunkasa Zirga-zirga

Masu ‘Adaidaita Sahu’ Sun Janye Yajin Aikin Da Suka Shiga A Kano

by Khalid Idris Doya
14 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim Kungiyar masu 'Adaidaita sahu' ta Kano ta...

Next Post
Fadar Shugaban Kasa Ta Gargadi Masu Yunkurin Batanci Ga Buhari

Fadar Shugaban Kasa Ta Gargadi Masu Yunkurin Batanci Ga Buhari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version