Khalid Idris Doya" />

Gwamnan Bauchi Ya Tallafa Wa Iyalan Wadanda Suka Rasa Rayukansu A Kifewar Kwale-kwale

Iyalan mutum 11 da suka rasa rayukansu sakamakon kifewar kwale-kwale a kogin Buji da Garin Dole da ke karamar hukumar Itas Gadau a kwanakin baya sun samu tallafin naira miliyan biyu daga hannun Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad domin rage musu radadi.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Abdullahi Maigari, shine ya shaida hakan a yayin rabon kudaden ga iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu sakamakon wannan iftila’in.

Maigari wanda ya shaida cewar kowani mutum daga cikinsu zai samu naira dubu dari (N100,000) na rage radadin halin da suka tsinci kai a ciki, ya kara da cewa al’ummomin da suka samu tallafin su sani ba wai diyyar asarar da suka yi ne aka biya su ba; a’a kawai tallafin rage radadi ne gwamnan ya ba su, sai shawarcesu da su dauki lamarin da ya faru a matsayin mukaddari daga Allah.

A cewarsa cikin kwanaki dari da ya yin a farko a matsayinsa na zabebben shugaban karamar hukumar, an samu aiwatar da muhimman ayyukan da suka dace wajen ganin an inganta rayuwar jama’a da suka kunshi, sashin wutar lantarki, ruwa mai tsafta, lafiya, ilimi, tallafa wa kungiyoyi, da agazawa kungiyoyin addinai tare da ‘yan kasuwa domin rayuwa take ingantuwa.

Da ya ke jawabi yayin rabon tallafin, Malam Magaji Gwaram ya nuna matukar godiyarsu ga gwamnan a bisa wannan tallafin da ya bayar, sai ya nemi wadanda aka ba su tallafin da su yi kokarin yin amfani da dukiyoyin ta hanyoyin da suka dace domin inganta rayuwarsu da na iyalansu lura da cewa da ‘yan uwansu na ciki za su ci gaba da aza musu, sai dai ya ce dukkanin abun da ya faru mukaddari ne daga Allah.

Idan za ku iya tunawa dai, jama’a 18 ciki har da iyaye mata ne suka rasa rayukansu sakamakon tsautsayin da ya faru na kifewar jirgin ruwa a cikin kogin Buji.

Exit mobile version