Gwamnan jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, ya amince da kashe naira miliyan sittin da biyu (62m) wajen samar da rancen gidaje wa malamai 220 da wasu ma’aikatan hukumar kula da malamai TSC wadanda ba malamai ba (Non Teaching).
Bayanin hakan na kunshe ne ta bakin shugaban hukumar kula da malamai, Hon. Babatunde Abegunde wanda ya fitar a ranar Litinin, ya shaida cewar rancen gidajen an samar ne wa ma’aikata 220 da suka kunshi malamai da wadanda ba malamai ba.
Abegunde, ya nuna farin cikinsu kan tallafin na gwamna Fayemi bisa wannan jin kan da ya yi wa malaman, a cewarsa cigaba da sake kudade wa tsarin samar da gidaje da motoci da gwamnati mai ci ke samarwa a matsayin rance na matukar taimaka wa malamai da ma’aikatansu.
Adegunde wanda ya kara da cewa kusan naira N340,754,231,74 ne daga watan Oktoban 2018 lokacin da gwamnati mai ci ta hau kan kara zuwa yanzu wanda mutum 2,459 suka samu cin gajiya zuwa yanzu.
“Ina jinjina wa gwamna bisa daukan matakin tabbatar da walwala da jin dadin ma’akata wadanda suka fuskanci matsatsin tattalin arziki sakamakon annobar Korona. Wannan rancen na taimakawa wajen warware wa ma’aikata kalubalen da suka fuskanta.
“Ina rokon wadanda har zuwa yanzu bas u samu amfanuwa da shirin ba, da su yi hakuri nan kusa suma za su amfana.”
Ya nemi ma’aikatan jihar da su cigaba da kula da ayyukansu tare da baiwa gwamnati mai ci hadin kai domin tabbatar da aiki na tafiya yadda ake so bisa inganci da nagarta.