Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya hori al’ummar yankunan karkara na jihar su sanya ido tare da kare aikin makamashin hasken lantarki ta makamashin hasken rana da ake musu don amfanin kansu.
Ya yi kiran ne a yayin kaddamar da aikin samar da wutar lantarki daga hasken rana mai karfin Kilowatt 85 a kauyen Dakkiti na karamar hukumar Akko.
Gwamnan ya kaddamar da aikin ne tare da babban Manajan Daraktan hukumar samar da wutar lantarki a yankunan karkara ta kasa (REA), Ahmed Salihijo Ahmed.
Wakilinmu ya nakalto cewa, Gidauniyar Gwamnatin tarayya kan samar da wutar lantarki a karkara (REF) ce ta gudanar da aikin, karkashin hukumar samar da Wutar Lantarki a yankunan karkara REA.
Gwamna Inuwa ya ce aikin alhaki ne na hukumar wanda ya dace da shirin Gwamnatin tarayya na kyautata rayuwar ‘yan Nijeriya da nausa ta gaba ta fuskar inganta wutar lantarki ga ‘yan Nijeriya, musamman ma wadanda ke zaune a yankunan karkara, yana mai fatan za a fadada irin wannan aikin zuwa sauran sassan jihar, kamar yadda wata sanarwar da Daraktan yada labaran gidan gwamnatin jihar, Ismaila Uba Misilli ta nakalto.
Inuwa na cewa, “Gwamnatinmu tana aiki kafada da kafada da Gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da dama don tabbatar da samar da ababen more rayuwa ga jama’a, musamman wadanda ke zaune a yankunan karkara”.
Sai ya ba da tabbacin cewa al’ummar jihar ba kawai za su goyi bayan wannan aikin ba ne, har ma za su marawa duk wasu ayyukan samar da lantarki, domin tabbatar da nasarar samar da dauwamammiyar wutar lantarki.
Gwamnan ya yi imanin cewa aikin zai yi tasiri wajen inganta rayuwar al’ummar yankin, “Ina yaba wa Gwamnatin Tarayya ta hanyar ma’aikatar Makamashi da kuma hukumar samar da lantarki a Karkara bisa jajircewa da gudummawar da suke bayarwa wajen samar da wutar lantarki ga al’ummomin mu mazauna karkara, muna ganin wannan kokarin naku a duk fadin kasar nan”.
Ya kuma bukaci al’ummar yankin su dauki aikin a matsayin nasu ta hanyar kiyaye shi daga mabarnata tare da tabbatar da suna biyan kudin wutar akan lokaci.
Gwamnan sai ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnati mai ci za ta ci gaba da samar da ababen more rayuwa ga mazauna karkara, musamman ganin cewa sama da kaso 75 cikin dari na al’ummar jihar suna zaune ne a yankunan karkara.
Manajan Darakta kuma shugaban hukumar samar da wutar lantarkin a karkara, Ahmed Salihijo Ahmed, ya ce kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sahale mata, hukumarsa ce ke da alhakin samar da makamashi ga al’ummomin Nijeriya da ba su da wutar ko basu wadatacciyar ta.
Ya ce an samu nasarar aiwatar da aikin ne a karkashin asusun samar da lantarki a Karkara wanda aka faro shi don tabbatar da daidaito wajen samarwa da rarraba wutar lantarki a fadin kasar nan.
Shugaban karamar hukumar Akko, Abubakar Barambu, ya ce bisa samar da wannar wuta ga al’ummar Dakkiti, a yanzu jama’ar kauyen za su iya morar alfanun da duk ake samu daga wutar lantarki ta fuskar ci gaban tattalin arziki.
“Ya ce ku sani cewa mun yi wannan aikin ne na Dakkiti bisa kyakkyawan tsari da bin ka’idojin kasa da kasa wajen kafa wannar karamar tashar wutar lantarki da aka girka kana mai karfin Kilowatts 85 wanda ya kunshi farantai masu tattara hasken rana guda 100, da batura 96 da kuma Injin Janareta mai karfin KbA 30.
Sarkin Gona, wanda ya samu wakilcin Ajiyan Gona, Alhaji Abubakar Usman, ya gode wa hukumar samar da lantarkin a yankunan karkara kan wannan karamci na gwamnatin tarayya tare da kara godewa gwamnati mai ci ta Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ke yi bisa jajircewa wajen tabbatar da gudanar da aikin a kan lokaci.