Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin 2026 na Naira biliyan 535,691,983 ga majalisar dokokin Jihar Gombe domin amincewa da shi.
Da yake gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin a gaban ‘yan majalisan a ranar Alhamis, Gwamna Inuwa ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 164.25 a matsayin kasafin gudanarwa na yau da kullum.
- Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani
- Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
An kuma ware Naira biliyan 371.44 don gudanar da manyan ayyuka.
Kasafin kuɗin, wadda aka yi wa laƙabi da “kasafin bunƙasa ayyukan ci gaba,” an tsara shi ne don ƙarfafa nasarorin da aka samu a baya-bayan nan da tabbatar da ɗorewar ci gaban rayuwar al’ummar jihar.
Gwamna Yahaya ya ce kasafin kuɗin na 2026 za a aiwatar da shi ne ta hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da suka haɗa da harajin da ake samu a cikin gida, da kason da ke zuwa daga gwamnatin tarayya, da na harajin VAT da sauran kuɗaɗen da ke zuwa daga asusun haɗaka na tarayya (FAAC).
Da yake ƙarin haske kan muhimman sassan da aka fi bai wa fifiko, Gwamnan ya bayyana cewa, ɓangaren tattalin arziƙi da ci gaban al’umma ne suka samu kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin, inda aka ware sama da Naira biliyan 269 don sanya hannun jari a muhimman fannoni.
Fannin ayyuka, gidaje da sufuri ne ke kan gaba da Naira Biliyan 135.9, sai ruwa, muhalli da gandun daji da aka warewa Naira Biliyan 88.4, yayin da noma, kiwo da ƙungiyoyin gama ya samu Naira biliyan 20.57.
A fannin harkokin zamantakewa, an ware Naira biliyan 80 don samar da ayyukan ci gaba da gina jama’a, inda ilimi ya samu Naira biliyan 31.9, yayinda ilimi mai zurfi ya samu Naira biliyan 17.5.
Ɓangaren kiwon lafiya ya samu Naira biliyan 25.9, wanda hakan ke nuna yadda gwamnati ke ci gaba da zuba jari wajen samar da lafiya mai inganci.
Fannin gudanarwa ya samu Naira biliyan 19.63, sannan ɓangaren doka da shari’a aka ware masa Naira biliyan 2.17, fannin filaye ya samu Naira biliyan 6.46; shi kuwa fannin Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido ya samu Naira biliyan 4.02.
Yayin da sashen matasa da ci gaban wasanni ya samu Naira biliyan 3.33; harkokin mata da ci gaban a’umma Naira biliyan 1.28; fannin yaɗa Labarai da raya al’adu kuwa Naira biliyan 10.38.
Gwamna Yahaya ya bayyana ƙididdigar kasafin kuɗin na 2026 a matsayin na ɗorawa kan ci gaban da gwamnatinsa ta faro na gudanar da shugabanci nagari, Gwamna Inuwa Yahaya ya yi ƙira ga majalisar akan ta yi nazari tare da ƙalailaice ƙudurin tare da sanya gudunmawa da tabarrukinta.
“Aikin dake gabanmu shi ne mu samarwa al’ummarmu kasafin kuɗin da zai wanzar da fatansu ya zuwa zahiri da kuma kyautata makomarsu,” in ji shi.
Kasafin kuɗin na 2026 ya dace da tsarin ci gaban Jihar Gombe (DEVAGOM) da kuma tsarin tattalin arziƙin ƙasa baki ɗaya. Da yake tsokaci kan harkokin tattalin arziƙi a dunƙule, Gwamnan ya ce sauye-sauyen da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɓullo da su, da suka haɗa da cire tallafin man fetur da sakin mara ga canjin kuɗaɗen waje, sun fara haifar da sakamako na ƙwarai.
A nasa jawabin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Gombe Rt. Hon. Muhammad Abubakar Luggerewo, ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya bisa yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da bin doka da oda, da gaskiya da kuma tsantseni wajen tafiyar da harkokin kuɗaɗen gwamnati.
Ya bada tabbacin duba kasafin akan lokaci da kuma gaggauta amincewa da ƙudurin kasafin na 2026.
Rt. Hon. Luggerewo ya kuma nuna jin daɗinsa da yadda jihar ke tafiyar da harkokin kasafin kuɗi, inda ya ce aiwatar da kasafin kuɗin 2025 ya samu nasarar fiye da kaso 60 cikin 100 ya zuwa ƙarshen watan Satumba, sannan ya yaba da yadda gwamnati ta samu ci gaba a fannin samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya, ilimi, masana’antu, da sabunta birane.
“Za mu ci gaba da tallafawa manufofi da tsare-tsaren dake tabbatar da zaman lafiya, inganta ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar jama’armu,” in ji kakakin.
A shekarar da ake ciki ta 2025, Gwamnatin Inuwa ta yi kasafi ne na fiye da Naira biliyan 369.9, inda daga baya aka yi bitarsa ya koma na fiye da Naira biliyan 451.6 biyo bayan samun ƙarin kuɗaɗen shiga fiye da yadda aka yi tsammani.














