Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnan Gombe Ya Jaddada Aniyarsa Ta Hada Kai Da Jami’an Tsaro

Published

on

Gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da yin aikin hadaka tare da bangarorin hukumomin tsaro domin tabbatar da cimma nasarar nan ta kyautata zaman lafiya da tsaro a tsakanin jama’an jihar.
Gwamnan ya yi bayanin ne a lokacin da yake kaddamar da gamayyar kwamitin bada shawara kan tsaro a tsakanin jama’a na tsarin ‘Community Policing’ da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar, kamar yadda kwafin sanarwar da Ismaila Uba Misali, Kakakin gwamnan Gomben ta shaida da ya fitar a shekaran jiya.
Gwamna Muhammad yana mai shaida cewa, muhimmin al’amari ga kowace gwamnati ta gari shine ta tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyar jama’anta, a bisa haka ne ya shaida cewar gwamnatinsa ta dauki matsayar kafa ma’aikatar kula da harkokin tsaron cikin gida da zimmar sanya ido kan lamuran da suka shafi tsaro da kalubalen da suke akwai domin tabbatar da inganta zaman lafiya.
Inuwa ya ci gaba da cewa jihar Gombe ta na morar dumbin ribar zaman lafiya a tsakanin jihohin da suke kewaye da ita a shiyyar arewa maso gabas, sai ya sha alwashin ci gaba da zage damtse domin tabbatar da wannan matakin na nan daram ba tare da barin matsalar tsaro ya samu wuri ba.
Sai dai ya shaida cewar akwai bukatar ci gaba da daukan matakan da suka dace lura da halin da shiyyar arewa maso gabas ke ciki kan matsalar tsaro da kuma abun da ke faruwa yanzu haka a shiyyar arewa maso yammacin kasar da ke fama da ‘yan bindiga.
Gwamnan ya na mai cewa tsarin tsaro na gamayya da ake yi da jama’an gari da jami’an tsaro (Comminity Policing) ya kunshi masu ruwa da tsaki da suka hada da jami’an tsaro, sarakuna, shugabannin addinai dana al’umma, tare da sauran bangarorin jama’a domin yin aiki tare don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
Gwamna Yahaya Inuwa, ya kalubalanci magidanta da suke jihar da su baiwa kwamitin hadin kai domin ya samu nasarar cimma manufar samar da shi, a cewar shi kwamitin da aka kafan ya kamata kowa da kowa ya ji nasa ne domin hada karfi da karfe wuri guda don tunkarar matsalar tsaro.
A cewar shi, tsarin gamayyar tsaron yana aiki tuntunin a sassan kasashe daban-daban, don haka ne ya shaida cewar jiharsa ma da take kan habakuwa da karin samun jama’a ba za ta zama na daban ba za ta bi matakin samar da tsaron domin tsaro yake inganta.
LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewar kwamitin masu bada shawara kan kwamitin gamayyar tsaron, ya kasance a karkashin shugabancin Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III da kuma Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Maikudi Shehu, da zai ke tsara inda lamarin zai tafi kana zai ke gabatar da rahoton halin da ake ciki wa gwamnan lokaci bayan lokaci.
Tun da farko a jawabinsa, shugaban ‘yan sandan Nijeriya, IGP Mohammed Adamu, wanda ya samu wakilcin AIG da ke kula da Zone 3, Halliru Abubakar Gwandu, ya shaida cewar tsarin ‘Community Policing’ ya kankama ne a shekarar 20204, inda Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta amshi tsarin a matsayin hanya mafi tsauki da zata inganta tsaro.
Ya na mai karawa da cewa tsaron rayuka da dukiyar jama’a na habakuwa da zama cikin aminci ne a duk lokacin da jama’a da suke cikin al’ummominsu suka ji za su shigo cikin lamarin tsaro don magance aiyukan ta’addanci da kare al’ummominsu.
AIG Gwandu, a cewar shi a kokarin shugaban ‘yan sanda na kyautata tsarin ya ingantata tare da daura tsarin bisa matakan zamani domin cimma nasara, inda yake mai bayanin cewa ta hakan ana samun sakamako mai kyau.
Da ya ke jawabin maraba, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Gombe, CP Ahmed Maikudi Shehu, ya shaida cewar rundunarsa tana jin dadin hadin kan da jama’a ke basu, a cewarshi da irin wannan hadin kan ne suke samun nasarorin wanzar da tsaro da kare rayukan jama’an jihar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: