Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamnan Gombe Ya Kaddamar Da Saida Takin Zamani 

Published

on

A kokarinsa na bunkasa sashin noma, gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya kaddamar da fara rabarwa da saida takin zamani domin ribantar daminar bana.
A lokacin da yake kaddamar da bikin a Gombe, gwamna Inuwa ya shaida cewar samar da takin cikin farashi mai rahusa kuma wadatacce ga manoma a dukkanin lokacin noma na daga ciki alkawuran da gwamnatinsa ta dauka a lokacin yakin neman zabe, inda ya shaida hakan a matsayin matakin cika alkawuran da ya dauka na bunkasa sashin noma a jihar.
A cewarshi, gwamnatinsa ta samar da tan-tan dubu 20,000 domin saidawa da rabawar ga manoma a kan lokaci domin su samu nasarar amfana da daminar bana duk da kalubalen da ake fuskanta kan yaki da Korona.
A cewarshi, tuni aka ware kaso mai tsoka da za a rabar ga manoma da suke fadin kananan hukumomi 11 a jihar don su ma su samu zarafin sayen takin cikin rahusa kuma a kan lokaci.
Gwamnan ya umurci a saida takin zamani samfurin NPK a kan kudi naira N5,000 a kan Kowace buhu guda daya, ya kuma kara da cewa, farashin sauran samfurin takin kamar Urea za a yi nazarinsa daga baya.
“Gombe ta samar da ton-ton dubu 20,000 na taki da za a saida wa manoma cikin farashi mai rahusa. Kai tsaye wannan na nuni da yanda muka himmatu ta fuskacin bunkasa harkokin noma a jihar nan.”
Ya ce, sun yi amfani da tsari mai nagarta da za su kai takin nan kai tsaye ga kananan hukumomin da suke jihar domin talawa su samu zarafin saye.
“Manufarmu ita ce don tabbatar da manomanmu na karkara sun samu zarafin mallakar takin nan domin su kyautata nomansu,”
Ya kuma kara da cewa gwwamnatin ta kafa kwamitin da zata bibiyi yadda aka saida takin tare da rabar da shi ga manoma wanda masu ruwa da tsaki da suka kunshi jami’an tsaro da sauransu suna cikin kwamitin.
Gwamna Inuwa Yahaya ya kuma nemi manoma da makiyaya da su maida hankalinsu wajen inganta danganta domin shawo kan matsalar fadace-fadace a tsakaninsu.
Tun da farko a jawabinsa, Kwamishinan gona na jihar, Hon. Mohammed Magaji, ya shaida cewar a kan umurnin da gwamnan ya basu, ma’aikatarsa ta fitar da tsare-tsare masu nagarta da takin zai je ga lungu da sako domin talakawa su amsa.
Hon. Magaji, yana cewa ma’aikatar gona ta jihar cikin shekara guda ta cimma nasarori masu gayar fa’ida da suka kai ga kyautata sashin noma da bunkasa harkokin dabbobi.
Daga nan sai gwamnan ya roki gwamnatin jihar da ta kara samar da karin jami’an gona ga ma’aikatarsu domin a cewarshi wasu da za su kammala aikinsu a shekara mai zuwa.
Advertisement

labarai