Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana kaduwa da jimaminsa bisa rasuwar dattijo, tsohon gwamnan jihar tsohuwar jihar Arewa Maso Yamma Alhaji Usman Faruk, Jarman Gombe.
Wakilinmu ya nakalto cewa, marigayi Usman Faruk dai tsohon kwamishinan ‘yan sanda ne, ya rasu ne a ranar Juma’a 18 ga watan Disamba bayan doguwar jinya da yayi fama da shi. An haifesa ne a shekarar 1935 a garin Gombe, ya zama gwamnan mulkin soja ne a yayin mulkin shugaban kasa a zamanin soja Yakubu Gowon
Gwamnan ya jagoranci tawagar gwamnatin da ta halarci jana’izar marigayin wanda aka yi a masallacin Modibbo Bubayero dake fadar mai martaba Sarkin Gombe.
A sakon sa na ta’aziyya da ya fitar ta hannun Kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, gwamna Inuwa ya bayyana marigayi tsohon kwanishinan ‘yan sandan a matsayin mutum mai cikakkiyar kima, jami’in tsaron da ya yi fice, wanda ya sadaukar da komai na shi don tabbatar da hadin kai da ci gaban Nijeriya, wanda kuma ya bar kyakkyawan abun tunawa da shi tsawon lokaci.
“Za mu yi ta tunawa da shi a matsayin shi na uba da nagartattun ayyukansa lokacin da ya ke cikin damara da bayan ritayarsa, musamman jajircewarsa ga hidimar al’umma, Jihar Gombe da Nijeriya baki daya a matakai daban-daban.
“A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, muna mika cikakkiyar ta’aziyyar mu ga iyalansa da abokai bisa wannan babban rashi. Allah ya yi masa sakayya da Aljannah Firdausi.”