Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kaddamar da Motoci da Babura da za a rabawa jami’ai da ma’aikatan sanya ido kan shirin kyautata rayuwan, da kuma Injunan ban ruwa ga manoman na rani.
Shirin tallafin, hadin gwiwa ne tsakanin gwamatin jihar da shirin na inganta noma da samar da tallafin kyautata rayuwa da ake kira (IBSDLEIP) a takaice, wanda ke karkashin kulawar bankin bunkasa ci gaban Afirka don tallafawa mata da matasa da gajiyayyu.
Sai ya bayyana farin ciki kan shirin, ya na mai cewa ci gaba abu ne da ake tsarawa da takamammiyar manufa ta bunkasa rayuwar al’umma musamman ma na yankunan karkara.
Ya ce, “Jama’ar mu da suka dogara ga har kar noma sun kai kaso 75 cikin dari na yawan al’ummarmu, don haka duk wani yunkuri na kyautata wannan sashi zai kance mai gwaggwaban tasiri akan jama’ar mu”.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnatinmu ta sanya azama sosai wajen aiwatar da wannan shiri, ta hanyar bada nata kason gudunmowa saboda sanin tasirin da zai yi ga mata da matarsa da marassa galihu.”
Don haka, “Ina shawartar wadanda za su kula da wadannan Motoci da Babura dama wadanda za su ci gajiyar wannan tallafi na Injunan ban ruwa da sauran kayan aiki, su tabbatar sun yi amfani da su yadda ya kamata, musamman ma wadannan motoci da suka kasance masu jan hankalin bata gari”.
Ya kara da cewa dole ne masu cin gajiyar wannan shiri su jajirce don ganin jama’ar jihar sun ci gajiyar wadannan kayayyaki.
Sai ya bada tabbacin gwamnatin sa na ci gaba da zakulo shirye-shirye da aiwatar da ayyukan da za su amfani al’ummar jihar.
A na shi tsokaci, Kwamishinan ruwa na jihar, Mijinyawa Yahaya, ya ce za a yi amfani da Motoci da Baburan ne wajen sanya ido kan aiwatar da shirin a jihar Gombe wanda aka sanya hanu akansa tun shekara ta 2016 amma aka yi watsi rashi saboda rashin kyakkyawar gudanarwa.
Ya ce sake farfado da shirin, na nuni da kyakkyawan jagorancin gwamna Inuwa wajen tafiyar da al’amuran jihar yadda ya kamata.