Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Gwamnan Gombe Ya Rattaba Hannu A Kasafin 2021 Na Biliyan N120.3

by Muhammad
December 24, 2020
in RAHOTANNI
2 min read
Rattaba
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya,

 

samndaads

Gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya rattaba hannu a kan kasafin kudi na 2021 domin ya zama doka da yawansa ya kai biliyan (N120,346,536,626.00) bayan da majalisar dokokin jihar ta amince da shi.

Kasafin wanda aka kara masa yawan kudi da ya kai naira (N682,680,000.00) wanda ya samu kari a kan daftarin naira biliyan (N119,663,856,626.00) da gwamnatin jihar ta aike majalisar tun da fari.

Da ya ke jawabi a yayin sanya hannu kan kasafin kudin a jiya a gidan gwamnatin jihar, gwamnan jihar Inuwa Yahaya ya shaida cewa an tabbatar da amincewa da kasafin ne bisa kyakkyawar hadin kai da ake samu tsakanin gwamnatin jihar da majalisar dokokin jihar

Ya ce, idan a ka yi nazari da shekarun baya, jihar ta na samun cigaba wajen gabatar da kasafin da kuma amincewa da shi a kan lokaci wanda hakan na nuna da cigaban da a ke samu ta fuskacin bada damar gudanar da ayyukan da za su ke kyautata rayuwar jama’an jihar.

Gwamnan ya yi amfani da wannan damar wajen gode wa al’ummar jihar a bisa hadin kai da goyon bayan da suke baiwa gwamnati mai ci tare da goyon bayan majalisar dokokin jihar ke bayarwa wajen amincewa da kasafin a kan lokaci tare da masa nazarin da ya dace, ya na mai cewa, “wannan na nuni da irin girman hadin hakai da ke tsakanin bangarorin gwamnati na zartaswa da na zana doka.”

Ya kuma bada tabbacin cewa gwamnati mai ci za ta cigaba da tabbatar da samar da tsare-tsaren da suka dace wajen kyautata rayuwar jama’a ta hanyar amfani da dan tattalin arzikin da jihar ke da su, gami da riritasu yadda ya dace.

A jawabinsa, Kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Abubakar Mohammed Luggerewo ya shaida cewar sun hanzarta yin aiki a kan kasafin da amincewa da shi ne lura da cewa inganta tattalin arzikin jihar da al’ummarta ne a gabansu.

Ya ce, kashi 52 na kasafin zai tafi ne wajen gudanar da manyan ayyukan raya jihar, yayin da kuma sauran ragowar kasafin kaso 48 cikin 100 zai tafi ne wajen gudanar da ayyukan yau da kullum, yana mai nuni hakan na fayyace irin yadda ake ajiye komai bisa muhallinsa wajen tabbatar da kyakkyawar shugabanci a jihar.

Kakakin ya kuma gode wa gwamnan jihar Inuwa Yahaya a bisa ayyukan da a ke shimfidawa da wadanda yake samarwa dukka domin cigaban jihar da al’ummarta.

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnan Sokoto Ya Kai Ziyarar Jajen Rasuwar Usman Faruk A Gombe

Next Post

Korona: Jihar Kwara Ta Kakaba Kulle Mai Sauki

RelatedPosts

Kwazon Tambuwal

Hobbasar Kwazon Tambuwal Na Fara Biyan Albashi Daga Haraji A 2023

by Muhammad
11 hours ago
0

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar, Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin...

Alan Waka

Aminu Alan Waka Ya Yi Bayani Game Da Sarautar Danburan Din Gobir

by Muhammad
11 hours ago
0

Daga Mukhtar Yakubu, A farkon shekarar nan ne ta 2021...

Jami'ar Bayero

Cibiyar Nazarin Dimokradiyya Ta Jami’ar Bayero Ta Nuna Rashin Gamsuwa Da Yadda Ake Gwamnoni Ke Gusanar Da Zaben Kananan Hukumomi

by Muhammad
11 hours ago
0

Daga Ibrahim Muhammad, Cibiyar nazarin Damakwaradiyya dake karkashin jami'ar Bayero...

Next Post
Kwara

Korona: Jihar Kwara Ta Kakaba Kulle Mai Sauki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version