Daga Khalid Idris Doya, Gombe
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta bada dukkanin goyon bayan da suka dace ga kafar yada labarai ta jihar GMC, don ba ta damar yin gogayya da sauran kafafen yada labarai a jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakwancin mambobin hukumar gudanarwa ta GMC karkashin jagorancin shugabanta, Muhammad Kabir Abdullahi a zauren majalisar zartaswa da ke gidan gwamnati, kamar yadda wata sanarwar da Daraktan yada labaran gwamnan, Alhaji Ismaila Uba Misilli ya nakalto mana.
Gwamnan ya bayyana hukumar gudanarwar ta GMC a matsayin mai matukar muhimmanci kasancewar kafafen yada labarai na jihar su ne bakin gwamnati wanda ke samar da labarai da shirye-shirye kan manufofi da ayyukan gwamnati ga jama’a don ci gaba da sanar da su abubuwan da ke faruwa a cikin Gwamnati.
Ya ce sanda aka darje aka zabo mambobin hukumar an kuma an nada su ne saboda yakinin cewa za su iya farfado da kafar yada labaran ya zuwa mafi nagarta kuma su rike ta da kyau don yin gogayya da sauran kafafe da kare muradun Gwamnatin Jihar.
Ya ce, “Ba za mu bari wani ya busa mana kakakin mu ba, dole ne mu busa da kanmu mu yi rawar mu yadda muke so.”
Gwamna Inuwa ya ce kalubalen da kafar ta GMC ke fuskanta kamar yadda shugaban ta ya gabatar akwai na gajere, da matsakaici da dogon zango, ya ce burinshi ne ya magance matsalolin gaba daya domin tashar ta kasance a kan kyakkyawan turba don aiwatar da ayyukanta ba tare da nakasu ba.
Ya ce, “Muna bukatar cikakken nazari game da kafar ta GMC. A shirye muke mu samar da duk kayan aikin da ake bukata da na gudanarwa. Duk wani ma’aikacin da ba a bukatar aikin sa a kafar ana iya tura shi wani sashi, don kar ya zama cikas maimakon mai taimakawa wajen cimma nasarar Gwamnati.”
Ya ce batun rarar ma’aikata ba wai kawai ya shafi kafar yada Labarai ta Gombe kadai ba ne, amma ga galibin Hukumomin Gwamnati, yana mai buga misali da ofishin kula da harkokin jihar Gombe da ke Abuja wanda ke da ma’aikata 72 kuma mafi yawansu ba su wani abu baya ga kasancewarsu a can.
“Kamar yadda ya ke a yau rabin kason kudin mu yana lafiya ne ga biyan albashi, wannan fa tun kafin a fara biyan Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi, yayin da muka fara aiwatar da shi kuwa, wasu fiye da naira miliyan 237 sun karu kan kudaden na albashi, ga kuma kudin tafiyar da Gwamnati ya karu saboda hauhawar farashi. Don haka duk abin da kuka taba kusan zai mai da mu kasa ne warwas.”
Ya ce al’amura sun kara tabarbarewa ne kasancewar Gombe ta na baya-baya wajen samun da kudaden shiga, yana mai cewa duk da cewa jihar tana samun ci gaba a kudaden shiga na cikin gida, amma har yanzu Gombe tana kasa sosai a fagen samar da kudaden shigan na ciki da waje.
Ya ce a baya Jihar ta ciyo bashi fiye da kima, ta yadda idan aka kwatanta bashin da yanayin kudaden shigan jihar wanda ofishin kula da basuka ke amfani da shi don tantance yadda kowace jihar za ta iya karbar bashi, na Gombe ya kai kaso 22.8 maimakon kaso 20 cikin 100 wanda ya ce yana zama cikas ga damar da jihar ke da shi na yiwo wani rance don gudanar da harkokinta.
Da ya ke bayyana tsarin farfado da gidan Rediyon, Shugaban Hukumar Gudanarwar kafar Watsa Labaran ta Gombe, Muhammad Kabir Abdullahi, ya ce wasu daga cikin kalubalen da gidan rediyon ke fuskanta sun hada da; rashin ingantaccen Janareta, da tsofin kayan aiki da Injuna da kuma gine-ginen da suka lalace.
Ya ce duk da yawan kalubalen da tashar ke fuskanta, mambobin hukumar gudanarwar sun taimaka a bangarorin bunkasa kwarewar fasaha da bunkasa hazakar ma’aikata da kayan aiki, girka na’urar magance tsawa, da samar da kyamarar zamani, da samar da damar wata shirye-shiryen kafar talabijin din jihar ta kafar watsa labaran tauraron dan adam ta Star Time da samar da makamashin hasken rana da dai sauransu.
A na sa jawabin, Darakta Janar na kafar yada labaran na Gombe, Kabiru Ibn Mohammed ya shaida wa Gwamnan cewa da zuwan sa kan karaga, ya samu tashar da kalubale iri-iri kama daga na ma’aikata da kayan aiki, yana mai cewa shugabannin hukumar gudarwar ta GMC a shirye suke wajen yin aiki da jajirtacciyar gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na sauya tashar da maidata abin kwatance.
Sai ya ba da tabbacin cewa kafar yada Labaran ta Gombe za ta cigaba da aiki a matsayin kafar yayata ayyuka da manufofin gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.