Daga Khalid Idris Doya,
Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya, ya nuna gamsuwarsa bisa yadda Zaben Kananan Hukumomin jihar ke gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da wani hargibi ba a halin yanzu.
Gwamnan wanda ya kada kuri’ar sa wajajen karfe 10:40am ya shaida wa ‘yan jarida jim kadan bayan jefa kuri’ar sa cewa jama’a sun fito kansu da kwarkwata su domin zabin ‘yan takarar da suke so.
Sai ya nemi jama’a da cewa su ci-gaba da bin matakan kariya daga Korona a yayin da suke jefa kuri’ar su, ya kuma ba su tabbacin samun adalci a sakamakon abun da suka kada.
“An yi tsarin da na tabbata duk abun da aka tsara zai zama alkairi ne ga al’umma jihar, Alhamdulillah”.
Gwamna Inuwa ya roki masu zabe da su kwantar da hankulansu da cewa za a tabbatar an ba su sakamakon zaben da suka zaba, ya hori masu zaben da su kasance masu bin matakan kariya daga cutar Korona domin kiyaye kai daga cutar Korona da ke yaduwa.
Ya kuma can daidai lokacin da Jama’a ke zaman jiran sakamakon zabensu su kasance masu da’a da kwantar da hankula gami da bin dokoki da ka’idoji.