Gwamnan Gombe Ya Yi Alhinin Rasuwar Abba Kyari

Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, ya nuna gayar takaici da jimamin rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Malam Abba Kyari wanda ya rasu a jiya Juma’a.

Gwamnan wanda ya shaida jimamin nasa ta cikin kwafin sanarwar manema labaru da babban hadiminsa kan hulda da ‘yan jarida Malam Isma’ila Uba Misili da ya fitar a yau, gwamna Inuwa ya ce, Kasar Nijeriya ta yi babban rashin nagartaccen shugaba, mai kishin kasa, mutumin kirki, wanda ya kasance a kowani lokaci mai kokarin sauke nauyin da ke kansa.

Gwamnan ya kara da cewa za a jima ba a mance da salon shugabancin na kwarai da marigayi tsohon shugaban ma’aikatan yayi ba, gami da aiki mai nagarta da ya aiwatar, sadaukarwa, biyayya da sallama wa kasa ta fuskacin sauke nauyin aiyukan da suke gabanshi tsawon lokacin da yayi yana aiki.

“A madadin gwamnati da al’umman jihar Gombe, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga shugaban kasa, iyalan mamacin, tare da gwamnati hadi da al’umman jiharsa ta Borno a bisa wannan babban rashin,” A cewar gwamna Yahaya.

Daga nan sai gwamnan yayi addu’ar Allah ya gabatar wa Abba Kyari ya sanya aljanna ta zama masa gida na karshe, ya kuma miqa ta’aziyyarsa ga al’umman Nijeriya gaba daya bisa wannan babban rashin da aka yi.

Idan za ku iya tunawa dai rahotonni sun bazu da ke tabbatar da cewar cutar Koronabairus ce ta yi ajalin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin wanda aka yi masa jana’iza da kaishi makwancinsa a yau Asabar.

Exit mobile version