Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana kaduwa da jimami bisa mutuwar Lauyan Jam’iyyar APC a Gombe, Barisra Abayomi Rotimi Williams wanda ya rasu ranar Alhamis din da ta gabata.
A sakon ta’aziyya da gwamnan ya fitar dauke da sanya hannun babban hadiminsa kan yada labarai Alhaji Ismaila Uba Misilli, Inuwa ya bayyana marigayin a matsayin kwararren Lauya, hazikin dan jam’iyya kuma babban jigo wanda ya yi rayuwa abar koyi wacce iyalansa da Jam’iyyar APC za su yi ta tunawa da su.
Gwamna Inuwa ya ce Barista rRotimi Williams ya bar tabbatacciyar damba a fannin biyayya, da jajircewa ga hidimar jam’iytar APC dama gwamnati mai ci.
Ya ce, “Barista Rotimi Williams ya tabbata dan rajin ci gaba, kwararren Lauya kuma fasihin dan siyasa da Allah ya yi wa baiwar basira, wanda za a yi ta kewar irin dimbin gudunmowa da basirarsa.”