Khalid Idris Doya">

Gwamnan Gombe Ya Yi Jimamin Rasuwar Shahararren Dan Kasuwa A.A Haruna

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya nuna kaduwarsa a bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa mai taimakon al’umma, Alhaji Ahmadu Haruna wanda ya rasu da safiyar Talatar nan da ta gabata a Gombe ya na da shekaru 84 a duniya.

Gwamna Inuwa wanda ya halarci jana’izar mamacin tare da mukarrabansa da ya gudana a harabar Masarautar jihar, ya misalta marigayi AA Haruna mai riko da addini, Shugaban al’umma kuma jigo da ya bar darasin koyi na hidimta wa jama’a tare da sadaukar da kai don su.
A sakon ta’aziyyarsa da ya fitar dauke da sanya hannun Ismaila Uba Misali, babban mai taimaka masa kan hulda da ‘yan jarida, Inuwa ya shaida cewa, “Mutuwa gaskiya ce kuma dole duk mai rai ya gamu da ita. Muna jajen rashin marigayi Alhaji Ahmadu Haruna wanda ya bada gagarumar gudunmawa wajen ginawa da ci gaban al’umma a lokacin da ya ke raye. Ya tafi ya bar abubuwan tunawa da shi, musamman kokarinsa na taimakon marasa karfi, taimaka wa addinin Musulunci da ci gaban al’umma”.
Gwamnan sai ya nemi iyalai da ahlin da ya rasu ya bar su da su yi kokarin koyi da kwawawan dabi’u na mamacin tare da ci gaba da koyi da su domin samun tsira duniya da lahira.
“A madadin gwamnati da al’umman jihar Gombe, Ina isar da sakon jajenmu da ta’aziyyarmu ga illahirin zuri’ar AA Haruna da al’umman Musulmi a bisa wannan babban rashin. Muna addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa tare da sanya Shi Aljannar Firdausi,” a cewar gwamnan.
Marigayi AA Haruna dai shahararren dan kasuwa ne a jihar wanda ya yi fice sosai a jihar.

Exit mobile version