Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Gwamnan Gombe Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Sanata Sa’ad Abubakar

by Khalid Idris Doya
January 17, 2021
in LABARAI
1 min read
Sanata Sa’ad Abubakar
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana alhini gami da jimamin rasuwar Sanata Sa’ad Abubakar Mohammed wanda ya rasu a ranar Juma’a ya na da shekaru 80 a duniya.

Sanata Sa’ad wanda ya wakilci yankin Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa daga 2003 zuwa 2007, har zuwa rasuwarsa shi ne Tafidan Deba.

Ta cikin sakon sa na ta’aziyyar da ya fitar dauke da sanya hannun Ismaila Uba Misilli, Babban Daraktan yada labaran gidan gwamnatin jihar Gombe, gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana marigayin kuma Dattijo a matsayin dan kishin kasa wanda ya kasance jajirtaccen ma’aikacin gwamnati, wanda ba za a taba mantawa da rawar da ya taka wajen ci gaban al’umma ba, a matsayin sa na dan majalisar tarayya dama kasance war sa dan kasuwa.

Ya ce, rasuwar tsohon Sanatan, babban rashi ne ba ga iyalan sa kadai ba, sai dai ma ga kasa baki daya.

Marigayin wanda ya kasance Injiniya a harkar sadarwa, ya bar mata daya da ‘ya’ya 7, an binne shi jiyan kamar yadda addinin Islama ya shimfida bayan masa sallar jana’izar da aka yi a babban Masallaci na kasa dake Abuja.

 

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Matan Tsofaffin Sojoji 200 Sun Samu Tallafi A Bauchi

Next Post

Gwamnan Gombe Ya Bukaci Malaman Jami’ar GSU Da Su Dakatar Da Shirin Shiga Yajin Aiki

RelatedPosts

An Yi Wa Mukarraban Buhari Rigakafin Cutar Korona

An Yi Wa Mukarraban Buhari Rigakafin Cutar Korona

by Khalid Idris Doya
7 hours ago
0

  Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ayau...

Farashin Gangar Danyen Man Fetur Ya Kai Dalla 71.28

Farashin Gangar Danyen Man Fetur Ya Kai Dalla 71.28

by Khalid Idris Doya
8 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim A karon farko a 2021, farashin mai...

Naira

Naira Na Shirin Sake Faduwa Warwas – FMDQ

by Khalid Idris Doya
15 hours ago
0

Za Ta Iya Kai Wa Dala 500 Cikin Mako Mai...

Next Post
Jami’ar GSU

Gwamnan Gombe Ya Bukaci Malaman Jami’ar GSU Da Su Dakatar Da Shirin Shiga Yajin Aiki

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version