Yusuf Shuaibu" />

Gwamnan Jihar Kebbi Ya Bukaci Maharba Su Kare Dabbobi

Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu, ya bukaci maharban Jihar su daina kashe dabbobi wadanda aka ayyana a kare su. Gwamnan ya bayar da wannan shawara ne ranar Litinin a Birnin Kebbi, lokacin da yake yi wa maharbar kananan hukumomi guda 21 na Jihar jawabi. “Gwamnati a shirye take ta ci gaba da taimaka wa kungiyar da kayayyakin ta suke bukara da kuma kudade domin karfafawa ‘ya’yan kungiyar. “Ina kira gare ku da ku daina farautar dabbobi wadanda aka ayyana a kare su.” in ji shi.
Ya yaba wa kungiyar maharba a kan yadda zu ka fito suka jifa kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya. Bagudu ya kuma bukaci maharban su taimaka wa jami’an tsaro wajen karfafa tsaro a Jihar. Ya gamsu da irin gudumawa da suka bayar a kan taimakawa rundunar Sharan Daji wajen wargaza maboyar ‘yan ta’adda, ya bukaci su bayar da irin dubarunsu.
Gwamnan ya bukaji maharban da su dunga sanarwa shugaban karamar hukuma, kafin su shiga yin faranta a dazuzzukan da ke makwabta da kasar nan.
Tun da farko dai, shugaban kungiyar maharban Jihar Mallam Bashir Mohammad, ya bayyana cewa sun gudanar da taro a filin wasa na Haliru Abdu Stadium, domin nuna goyan bayan su ga wannan gwamnati da kuma jam’iyya mai mulki.

Exit mobile version