Gwamnan Jihar Nasarawa Ya Bayyana Damuwarsa Kan Biyan Albashin Ma’aikata

albashin

Daga Zubairu M Lawal,

Gwamna Abdullah Sule na Jihar Nasarawa ya nuna damuwa kan yadda akayiwa Ma’aikatan Gwamnatin jihar biyan albashin jeka da halinka.

Gwamnan ya ce abin ta kaici anayiwa Ma’aikatan Gwamnatin jihar biyan albashi kashi kashi ko kashi daya bisa dari.

Ya ce ba ya jin daɗin biyan albashi a cikin kashi ɗaya bisa ɗari saboda a duk tsawon rayuwarsa ya kwashe kusan wacce shekara 30, yana aiki bai taɓa karɓar albashin nasa a kashi kashi ba.

Gwamna Abdullah Sule ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da da masu kula da bangaren kudi na jihar da suka hada tsofin dakatatun Daraktocin Gudanar da Ma’aikata (DPMs) da na Kudi da (DFAs) a gidan Gwamnati.

Gwamnan ya ce ba zai samu kwanciyar hankali ba matukar yana ganin Ma’aikatan Gwamnati na karban albshi kashi-kashi.

Gwamnan ya jaddada cewa wannan shine karo na farko da ya gana da tsofin masu kula da bangaren kudi na sha’anin mulki tun bayan da aka dakatar da su. Kuma yanzu ya gayyato sune domin jin ta bakinsu saboda ya gano yadda za a warware wannan matsalar ba tare da cutar da kowa ba.

Gwamnan ya ce tsarin Gwamnatin sa ta baiwa Kananan Hukumomi damar cin gashin kanta ta rika aiwatar da duk abubuwan da ya rataya a wuyarta. Amma ba zai ji dadi ba ace Ma’aikatan Kananan Hukumomi suna cikin halin kunci a fannin albashi.

Ya ce, a kullum idanuwa na na kan lamurar abubuwan da suka shafi Ma’aikatan Gwamnati domin burina naga komai na tafiya dai dai amma sau dayawa ana samun akasin hakan.

Ya kara da cewa tsawan watanin biyu da aka dakatar da masu kula da bangaren Kudi saboda matsalolin batun biyan albashin ma’aikatan Kananan Hukumomi. Duk da cewa tafiyar taku bai amfanar da warware matsalolin ba.

Gwamnan ya bukace su da su baiwa kwamitin da aka kafa hadin kai domin gano yadda za a warware matsalolin dake addabar albashin Kananan Hukumomi.

Exit mobile version