Connect with us

LABARAI

Gwamnan Jihar Yobe Ya Shirya Takarar Sanatan Shiyya Ta Daya

Published

on

Babban Daraktan yada labarai a ofishin gwamnan jihar Yobe, Malam Abdullah Bego ya bayyana cewa, a cikin kibtawa da bisimillah, gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam zai tumurmusa Sanatan shiyya ta daya (Zone A) a jihar; sanata Bukar Abba Ibrahim, wajen samun tikitin amincewar yin takara a babban zaben 2019 mai zuwa.
Bego ya bayyana cewa, “Gaidam babban jigo ne kuma jagora a jam’uyyar APC wanda hakan zai bashi gagarumin rinjayen samun amincewa wajen tsayawa takarar kujerar sanatan yankin, kana kuma idan an yi ka’akari da ayyuka masu ma’ana da ya shimfida a jihar Yobe baki daya”.
Baya ga haka kuma, ya ce, ai tun da jimawa jama’ar yankin, suka dawo daga rakiyar sa tare da yanke shawarar yiwa sanatan- tsohon gwamna, mai zango na uku a zauren majalisar dattijai, ritaya, domin ya dawo gida haka nan.
Abdullah Bego ya yi wadannan Bayanan ne a karshen wannan mako, wanda ake kallon martani ne, biyo bayan wani ikirari da tsohon gwamnan, Sanata Abba Ibrahim ya yi, inda ya nuna cewa shi ‘ubangidan siyasar’ Gwamna Gaidam ne, sannan kuma ‘fitila’ a gare shi- a siyasance.
Mai magana da yawun gwamnan, ya ce, Sanata Abba Ibrahim “Bai taba zama ubangidan siyasa ga gwamnan jihar Yobe ba”, wanda ya hakikance kan cewa, Alhaji Ibrahim Gaidam zai gudanar da sha’anin siyasar sa cikin nasara, tare da kayar da Sanata Bukar a cikn sauki.
“Abu ne a sarari; tarwai, ga duk mai bibiyar siyasar jihar Yobe kan cewa, Gwamna Gaidam ba shida wani ubangida. Sannan kuma babu yadda Bukar Abba zai kasance abin koyi a siyasa ga Gaidam. Sanin kowa ne kan cewa Gwamna Gaidam dan siyasa ne mai cin gashin kan sa, kuma wanda ya fara kada ta tun daga matakin farko, wanda ya samu cikakken goyon bayan jama’ar sa, wajen zaben sa har karo biyu, ba kamar Bukar Abba ba”.
Bego ya nanata cewa, ai fifikon da ke tsakanin Gaidam da Bukar, ba kadan ba ne. “a ma bar zancen rata a tsakani- a cikin sauki Gaidam zai tika Bukar Abba kasa, muddin ya yi gigin bayyana aniyar sake neman a zabe shi a kujerar sanatan zone ‘A’. Sannan kuma, da ace zai girmama kalaman sa, da ban zaci ya zai waiwayi batun sake takara ba, saboda yadda a baya ya riga ya bayyana cewa ba zai tsaya takara ba, matukar idan Gaidam ya nuna sha’awar sa”.
“Ina mai tabbatar maka da cewa, mutane sun kagu sosai, suna jiran lokaci ya yi domin dakatar dashi daga wakili a zauren majalisar dattijai ta kasa, a babban zaben 2019 mai zuwa, tare da kwana cikin shirin maye gurbin sa da Gwamna Gaidam, wanda ya cika musu alkawurran da ya dauka- wajen shimfida musu ayyukan raya al’umma”. Inji Malam Bego.
Advertisement

labarai