Gwamnan Kaduna Ya Kare Shirinsa Na Sulhu Da 'Yan Bindiga
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Kaduna Ya Kare Shirinsa Na Sulhu Da ‘Yan Bindiga

byKhalid Idris Doya and Sulaiman
8 months ago
Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya yi bayanin dalilin da ya sanya gwamnatin jihar ta yanke shawarar tattaunawa da ‘yan bindiga, ya ce, hakan ya fi kan a yi ta asarar rayuka.

A cewar gwamnatin, iyalan wadanda abin ya shafa ne kawai za su fi fahimta matakin yadda ya kamata har ma su yi godiya kan dalilin da ya sa gwamnati ta dauki wannan mataki mai muhimmanci.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba
  • Gwamnatin Katsina Ta Fitar Da Naira Miliyan Dubu 50 Domin Samar Da Ruwan Sha 

Gwamnan a hirarsa da sashin Hausa na BBC wanda wakilinmu ya bibiya, Gwamna Sani ya yi karin haske kan dalilan da suka sanya gwamnatinsa ta zabi sulhu na zaman lafiya da ‘yan bindiga da suka addabi wasu yankunan jihar.

LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa Jihar Kaduna dai na ci gaba da fama da hare-haren ‘yan bindiga a wasu kauyuka, musamman a cikin kananan hukumomin Chikun, Kagarko, Giwa, Kajuru, da Birnin Gwari, kari kan yawan kai farmaki manyan hanyoyi da yin garkuwa da mutane lamarin da ke janyo asarar rayuka da dimbin dukiya.

Gwamnan ya ce, “Mutanen da lamarin ta’addancin ya shafa sun yi kira ga a yi sulhun. A misali, Sarkin Birnin Gwari ya yi kira da irin wannan sulhun.

“Da na tambaye shi dalili, sai ya ce al’ummominmu suna fama da barnar ‘yan bindiga da hakan ke janyo asarar rayuka da garkuwa da mutanenmu tsawon shekaru zuwa yanzu ba tare da samun mafita da shawo kan lamarin ba.”

Gwamnan ya ce bayan rokon, ya zauna da masu ruwa da tsaki ciki har da mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, kafin daga karshe suka amince da fito da shirin yin sulhun.

Ya kara da cewa matakin na zuwa ne bayan da ‘yan fashin dajin suka sako mutane 200 da suka yi garkuwa da su a kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari. Gwamnan ya nuna fatansa na cewa matakin zai dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta yadda manoma za su sami damar komawa gonakansu domin yin noma da kuma dawo da harkokin kasuwanci yadda ya kamata.

“Gara na yi sulhu da ‘yan bindiga da ran mutum daya ya salwanta. Idan ba haka ba, ni ne zan je gaban Allah na yi bayanin wannan rasa ran domin na rantse cewa zan kare rayukan mutane,” ya shaida.

Kazalika, ita ma kungiyar Dattawan Arewa (ACF), ta shelanta cikakken goyon bayanta ga matakin Gwamna Uba Sani na yin sulhu da zaman lafiya da ‘yan bindigan a Kaduna da ma yankunanta.

A hirar da ya yi ta wayar salula da LEADERSHIP, jami’in watsa labarai na kungiyar ACF, Farfesa T.A Muhammad Baba, ya ce kungiyar ta yi maraba da yunkurin gwamnan na kawo karshen garkuwa da mutane da aikace-aikacen ‘yan fashin daji.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu
Siyasa

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Next Post
Ƙarar Kwana: Yadda Hakimin Kaduna, Sarkin Yaƙin Zazzau Ya Faɗi Ya Rasu

Ƙarar Kwana: Yadda Hakimin Kaduna, Sarkin Yaƙin Zazzau Ya Faɗi Ya Rasu

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version