Gwamnan Nasarawa Ya Gabatar Da Kasafin Kusan Naira Biliyan 113

Kasafin

Daga Zubairu M Lawal

A jiya Talata ne Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullah Sule, ya kaddamar da kasafin kudi na shekara ta 2021 da adadinsa ya kai Naira Biliyon 112,923,174,543 a gaban Majalisar Dokokin jihar da ke garin Lafia.

Kasafin kudin shekarar 2021 da a ka yi wa lakabi da kasafin farfado da tattalin arzikin jihar.

Kasafin zai shafi manyan ayyuka da kananan da karashen ayyukan da Gwamnatin ta fara a shekarar 2020 dama wanda tsohuwar Gwamnatin da ta shude ta fara ba ta karasa ba.

Bangaren Ilumi da kimiyar zamani ta ICT zata lashe sama da 35.4 biliyon, sai fannin tsaro da zai lakube 14.3 biliyon domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa da tsare dukiyar al’umman jihar.

Bangaren Majklsa zasu samu 2.7biliyon, hakama fannin Shari’a da ma’aikatan ta 3.8 biliyon. Fannin kiwon lafiya zai samu 11.4 bilyon. Harkan noma da Ruwan sha mai inganci 6.5 biliyon. Bangaren tsaftar Muhali ta jihar zata samu 10.4 biliyon.

Haka zalika akwai kwmmala gyaran tashar motar zamani ta Karamar Hukumar Karu wanda zai lakube 1000,000,000 hakama tashar mota ta zamani wanda ake ginawa a garin Lafia zai lakube 700,000,000.

Hanyar Mararaba-Udege zai samu 1000,000,000, domin kammalawa sannan filin sauka da tashin jirgin sama dake Lafia na bukatar 700,000,000.

Babban titin da ya ratsa katangan gidan Gwamnati zuwa Akurba zai lakube 1,300,000,000 da dai sauransu.

Gwamnan ya ce kudaden ana saran za a same su ne ta hanyoyi daban dabam da suka hada da kudaden harajin da ake karba a jihar.

Da kuma kudaden da ke shigowa daga asusun Gwamnatin tarayya. Da wanda ake saran rantowa idan yuhuwar hakan ya samu.

Gwamnan ya baiwa fannin ilumi fifiko a kasafin kudin shekarar 2021 domin samu. Ilumi mai inganci ga matasan jihar Nasarawa.

Da yake karban kasafin, Kakakin Majailas Dokokin jihar Honorabul Balarabe Abdullah ya jinjinawa Gwamna Abdullah Sule saboda yadda yake gudanar da cigaba a jihar Nasarawa.

Kakanin majalisar ya yabawa Gwamnan jihar Nasarawa kan yadda yake tafiyar da al’umman cikin harkokin Gwamnatin sa.

Ya Kuma yabawa matasan jihar kan yadda matasan jihar saboda yadda suka ki sanya kansu cikin rigimar zanga zangar End#sasr. Kakakin majalisan ya yabawa Shugaban kasa Muhammad Buhari saboda yadda yake bunkasa harkokin cigaban matasa da kawo sauyi mai kyau ga al’umman Nijeriya.

 

Exit mobile version