Gwamnan Nasarawa Ya Nada Shugabannin Hukumar Hajji Da Na Hukumar Ziyarar Kirista

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya nada Mustapha Yahuza-Musa a matsayin sabon shugaban hukumar lura da aikin Hajji da walwala na Musulmi, a yayin da kuma ya nada David Ayewa a matsayin Babban Sakataren gudanarwa na hukumar masu ziyarar Kirista.

Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Tijani Ahmed, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Alhamis a garin Lafia na jihar.

Ahmed ya yi bayanin cewa an sanya Ayewa ne bayan an cire Musa Aloko a mukamin. Ya tabbatar da cewa; nada sabbin shugabannin hukumomin ya faru ne a wani mataki na gwamnati na inganta hukumomin.

Sakataren gwamnatin ya ce; har wala yau an nada Rabaran Markus Shammah a matsayin shugaban hukumar ziyarar Kiristan, a yayin da aka nada Mustapha Yahuza-Musa a matsayin shugaban hukumar aikin hajji ta Musulmi.  

Sauran membobin hukumar ziyarar Kirista din sun hada da; Grace Mathias Chingon, Jonathan Joseph Jame, Rabo Dakare da Rabaran Fr. George Shenge.

Ahmed ya tabbatar da nadin Hajiya Aishatu Ibrahim Madayana, Umar Usman Baba, Idris Mohammed Umar, Alhaji Liman abdullahi Gabas, Ibrahim Bala Moskolo da Alhaji Musa Turaki a matsayin membobi a hukumar aikin hajji ta Musulmi ta jihar.

Exit mobile version