Gwamnan Nasarawa Ya Raba Wa Manyan Sarakuna Motoci 25

Daga Zubairu M Lawal Lafia

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su kara kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a cikin jihar.
Gwamna ya bayyana hakane sa’ilin da yake mika motoci na alfarma ga sarakunan gargajiya masu daraja ta daya su 25 cikin kananan hukumomi 13 da ke fadin jihar.
Gwamna Abdullah Sule ya ce baiwa Sarakunan Gargajiya motocin ya tabbatar da kwazonsu na taimakawa Gwamnatin jihar wajen tsaro da bunkasa tattalin arzikin jihar Nasarawa.
Gwamna yayi kira ga sauran Sarakuna masu mukamin Daraja ta biyu zuwa ta uku da su zauna da shirin suma tasu na nan tafe.
Ya ce; Gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin cigaban al’umman jihar Nasarawa ta hanyoyin bunkasa sana’o’i da dogaro da kai domin samun yalwataciyar tattalin arzikin jihar Nasarawa.
Gwamnan ya yabawa Bangaren Jami’an tsaro saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Shugaban Karamar Hukuma Lafia kuma jagoran Shugabannin Kananan Hukumomin jihar Nasarawa Alhaji Aminu Mu’azu Maifata ya yaba wa Gwamna Abdullah Sule bisa kokarin da yakeyi na martaba Sarakuna iyayen kasa.
Ya ce; wannan babban cigab ane wanda zai karawa Sarakunan kwazo wajen tabbatar da zaman Lafia da cigaban jihar Nasarawa.
Jerin sunayen Sarakunan da suka amfana da Motocin sun hada da: Sarkin Lafiya, Sarkin Keffi, Sarkin Doma, Sarkin Kwandare, Sarkin Awe, Baga Toni, Rindir, Sarkin Azara, Sarkin Keana, Zee- Migili, Ajiri, Babye da Nyankpa.
Sauran su ne: Sarkin Obi, Sarkin Nasarawa, Are – Eggon, Sarkin Karshi, Obanda, Sarkin Karu, Gom- Mama da Sarkin Loko. Sai dai akwai sauran uku wadanda motocin nasu ba su karaso ba.

Exit mobile version