Muhammad Awwal Umar" />

Gwamnan Neja Ya Bi Sahun Maniyyatan Jiharsa 527

Gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bar Minna, fadar gwamnatin jihar, tare da maniyyatan jihar 527, don aikin Hajji na 2019 a Kasa Mai Tsalki.

A lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a babban filin jirgin sama ta Minna, ya ce, zai tafi aikin Hajjin ne tare da maniyyatan jihar ne, domin sanin halin da maniyyatan jihar ke fuskanta a lokacin aikin Hajjin, don karfafa masu gwiwa a duk lokacin da aikin ya zo.

“Tun lokacin da na zama gwamna a shekarar 2015 ban tafi aikin Hajji da mahajjatan jiha ta ba. Ina son sanin yadda su ke ji da kuma yadda a ke yi mu su jagoranci a Kasa Mai Tsalki.

Na karbi rahotanni daga kwamitoci daban-daban, amma na yanke hukuncin a wannan karon zan tafi tare da su dan ganarwa ido na yadda abubuwan ke gudana idan akwai bangaren da ke bukatar kulawar gaggawa sai mu mayar da hankali kafin wani aikin mai zuwa.

Gwamnan ya ce, idan mun isa kasa mai tsalki, zamu addu’o’i kan matsalar tsaro, samun zaman lafiyar kasa da jiha, cigaban tattalin arzikin jihar da kasa baki daya.

Da yake karin haske, Amirul-Hajjin bana, Injiniya Inuwa Musa Kuta, yace hukumar jin dadin alhazan jihar (NSPWB) ta kara alawus na jami’an jin dadin alhazai ( APWOs) ta yadda za su ji dadin gudanar da aikin yadda ya da ce.

Ya jawo jami’an APWO da su zama jakadu na gari wajen jagorantar mahajjatan da su kan su mahajjatan wajen bin dokokin kasar Saudiya sau da kafa, domin samun gudanar da aikin Hajji karbabbe.

A nashi bahasin kuwa, sakataren rikon na hukumar jin dadin alhazan, Alhaji Umar Makun Lapai, yace Mahajjata 3273 ne hade da shugabannin jihar zasu sauke faralin hajji ba na daga jihar Neja.

Ya ce, gwamnatin jiha ta shirya ciyar da mahajjatan jihar sau uku a yini, wanda wannan irin sa ne a karon farko, tare da Babban cibiyar kula da lafiyar mahajjatan a daya daga masaukarsu a Kasa Mai Tsalki.

Sakataren rikon yace an samu cigaba sosai a wannan shekarar a bangaren bizar inshora ta wannan shekarar,  da ya juya kan tsaikon da ake samu na jinkirin tashin jirage kuwa, ya jawo hankalin gwamnatin tarayya da cewar ya kamata da tai dubi akan wannan lamarin na rashin samar da jirage kan kari wanda hakan ke sa ana samun tsaikon tashi kan kari.

Exit mobile version