Shugaban kungiyar gwamnonin arewa ta tsakiya, gwamna Abubakar Sani Bello ya taya gwamnan Kaduna Mallam Nasir El-Rufa’i murnar cika shekaru sittin da daya da haihuwa.
Gwamnan ya bayyana sakon taya murna a wani sakon da jami’ar yada labaransa ta aikewa manema labarai talatar makon nan, inda ya bayyana cewar Mallam Nasiru El-Rufa’i a matsayin wanda ya taka rawar gani wajen cigaban tattalin arzikin Najeriya baki daya.
Gwamnan yayi addu’ar Allah ya cigaba da baiwa takwaran nasa na jihar Kaduna lafiya da kwarin guiwa dan cigaban jihar Kaduna da kasa baki daya.
“Kana da yanayin zama cikakken dan Najeriya na kwarai bisa la’akari da irin shugabancin da ka ke ta hanyar jajircewar ka bisa gaskiya da amana.
“Ina taya ka murnar cikar ka shekaru sittin da daya a duniya da haihuwa, inai ma addu’ar Allah ya kara ma tsawon rayuwa, kwarjini da lafiya, da cigaba mai dorewa”, a cewarsa.