Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya taya Rabi Umar murnar samun mukamin kwamishiniyar ‘yan sanda a rundunar ‘yan sanda ta kasa.
Gwamnan ya taya kwamishiniyar ne a lokacin da ta ziyarce shi a masaukin gwamnatin jihar da ke Abuja.
Gwamnan yayi farin cikin jajircewar da tayi har ta cin ma wannan matsayin wanda a cewarsa ba nasarar ta ba ce ita kadai, nasarar jihar ce gaba daya na kasancewar ta kwamishiniya mace ta farko a jihar.
Abubakar Bello, ya bukace ta da kara jajircewa wajen yin aiki tukuru domin samar da sakamako mai kyau, wanda zai karawa sauran matan jihar kwarin guiwa.
A bayaninta, kwamishiniya Rabi Umar ta baiwa gwamnan tabbacin ba za ta baiwa jihar kunya ba, za ta tabbatar tayi abinda zai kare mutuncinta da jihar baki daya tare da nuna farin cikinta akan kwarin guiwar da gwamnan ya ba ta.
Rabi Umar, ita ce kwamishiniya mai kula da bangaren ilimi a Abuja kuma tana auren mataimakin shugaban rundunar ‘yan sanda ( AIG) mai ritaya Umar Abubakar Manko daga karamar hukumar Bida a jihar Neja.