Gwamnan Oyo Ya Nemi Iyaye Su Muhimmantar Da Ilimin ‘Ya’yansu

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya shawarci iyaye da su muhimmantar da ilimin ‘ya’yansu da wadanda suke riko.

Makinde ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Cocin St. Paul Anglican Church, dake Yemetu a garin Ibadan a yayin taron addu’a karo na 80 wanda Abigael Makinde, mahaifiyar gwamnan ta shirya.

Gwamna Makinde har wala yau ya shawarci iyaye da masu rikon ‘ya’ya su bai wa ilimin ‘ya’yansu muhimmanci domin samar wa da ‘ya’yansu kyakkyawan fata a nan gaba.

Har wala yau gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta tabbata ta samar da tsarin samar da ingantaccen ilimi a dukkanin makarantu gwamnati a matakin Firamare da Sakandare dake fadin jihar, inda ya ce hakan zai nuna muhimmanci ilimi.

 

Exit mobile version