Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da aikin gina gidaje 500 a ranar Talata, aikin da zai ci naira biliyan 22 domin rage matsalar ƙarancin gidaje a jihar.
Gwamnan ya ce wannan aiki yana cikin shirin gwamnatinsa na inganta rayuwar jama’a da kuma gyara birane.
- KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano
- Bilicin: NAFDAC Ta Kama Mutane 6, Ta Rufe Shaguna A Kano
Aikin zai haɗa da gidaje 300 masu ɗakuna uku da kuma gidaje 200 masu ɗakuna hudu.
Ya bayyana cewa lokacin da ya hau mulki, gwamnati ba ta da gidaje nata, don haka za a sayar da waɗannan gidaje ga ma’aikata da talakawa a saukakakken farashi da tsarin da zai amfanar da su.
Za a kammala aikin cikin wata 12 a unguwar Wajake da ke ƙaramar hukumar Wamakko a sabon birnin Sakkwato.
Gwamnan ya buƙaci kamfanin da ke aikin da ya yi aiki mai kyau kuma ya kammala a kan lokaci.
Ya ce dole ne a gina gidajen cikin inganci domin taimakawa wajen rage matsalar rashin gidaje da jama’a ke fuskanta a jihar.